Kwankwaso, GEJ, Osinbajo, Atiku: ‘Yan siyasan da har yau ba su ce komai a kan 2023 ba

Kwankwaso, GEJ, Osinbajo, Atiku: ‘Yan siyasan da har yau ba su ce komai a kan 2023 ba

  • Yayin da aka dumfarar 2023, ‘yan siyasa da-dama su na ta bayyana manufarsu ta tsayawa zabe
  • Sai dai kuma akwai wadanda har yanzu ba su bayyana inda suka sa gaba ba, har zuwa yanzu haka
  • Daga cikin wadanda suka bar magoya bayansu a cikin duhu akwai mataimakin shugaban kasa

Legit.ng Hausa ta kawo jerin wasu daga cikin ‘yan siyasar da har yanzu an rasa gabansu:

1. Goodluck Jonathan

Rade-radi sun dade su na yawo cewa tsohon shugaban kasa, Dr. Goodluck Jonathan zai sauya-sheka zuwa jam’iyyar APC, har a ba shi takarar shugaban kasa a zaben 2023.

Goodluck Jonathan bai fito ya musanya wannan rade-radi ba, ya kuma yi gum da bakinsa a kan batun siyasar 2023. Har yanzu masoyansa ba su san matsayar da yake kai ba.

Kara karanta wannan

Sabon lale: Atiku ya jefar da abokin takararsa, zai zabi Gwamnan PDP ya yi masa mataimaki

2. Yemi Osinbajo

Mataimakin shugaban kasa, Yemi Osinbajo ya na cikin wadanda ba su bayyana manufarsu ba. Osinbajo bai fadi ko zai nemi takarar shugaban kasa, ko ba zai nema ba.

Hadiman shugaban kasa, Sanata Babafemi Ojudu ya ce kwanan nan za a ji daga bakin Farfesa Osinbajo, kawo yanzu dai mataimakin shugaban kasan bai ce uffan ba.

Osinbajo, Atiku
Yemi Osinbajo da Atiku Abubakar Hoto: www.ripplesnigeria.com
Asali: UGC

3. Atiku Abbubakar

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Alhaji Atiku Abubakar bai fito a mutum ya bayyana nufinsa na takarar shugabancin Najeriya ko akasin hakan a zaben da za ayi a 2023 ba.

A jiya ne aka ji cewa jigon na jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar ya kai ziyara wajen tsohon shugaban kasa, Janar Ibrahim Babangida inda wasu ke ganin ya fara shirin neman takara.

4. Rabiu Musa Kwankwaso

Kara karanta wannan

2023: Jerin abubuwa 6 da za su tare hanyar Atiku Abubakar ya zama Shugaban Najeriya

Daga cikin wadanda ake ganin su na neman takarar shugaban kasa a Najeriya, Rabiu Musa Kwankwaso yana cikin wadanda ba a san inda suka sa gaba a zaben 2023 ba.

Tsohon gwamnan na Kano ya ce zai yi magana a lokacin da ya dace, har yanzu ana sauraronsa. Bisa dukkan alamu Kwankwaso yana nazari ne kafin ya dauki wani mataki.

5. Nyesom Wike

Shi ma Gwamna Nyesom Wike bai bada tsayayyar amsa a kan maganar takarar shugaban kasa a 2023 ba. Ana tunanin gwamnan na Ribas yana harin tikitin jam’iyyar PDP.

Sauran ‘yan siyasan da suke cikin wannan jeri sun hada da tsohon gwamnan Jigawa, Sule Lamido da tsohon ‘dan takarar shugaban kasa a PDP, Kabiru Tanimu Turaki.

Asali: Legit.ng

Online view pixel