Tinubu, Saraki, Okorocha da ‘yan takaran Shugaban kasa 6 da EFCC da ICPC suke bincike

Tinubu, Saraki, Okorocha da ‘yan takaran Shugaban kasa 6 da EFCC da ICPC suke bincike

  • ‘Yan siyasar Najeriya da-dama sun fara fitowa su na bayyana shirinsu na neman kujera a zaben 2023
  • A cikin wadanda suke harin zama shugaban kasa a zabe mai zuwa, akwai wadanda ake zargi da laifi
  • Zargin da ke kansu sun hada da karya wajen bayyana kadarorinsu, satar dukiyar gwamnati da sauransu

Binciken ICIR ya nuna daga cikin shahararrun wadanda suka bayyana burin tsayawa takarar shugaban kasa a 2023, akwai masu kashi a gindinsu.

Akwai wadanda alamu su ka nuna za su iya neman mulki, amma akwai bukatar su wanke kansu a gaban hukumomin EFCC, ICPC, CCT, ko an shiga kotu.

Ga wasu daga cikinsu:

1. Anyim Pius Anyim

Tun a 2021 Sanata Anyim Pius Anyim ya ce zai yi takarar shugaban kasa, amma EFCC ta na zarginsa da laifin rashin gaskiya da cin kudin al’umma.

Kara karanta wannan

2023: Jerin abubuwa 6 da za su tare hanyar Atiku Abubakar ya zama Shugaban Najeriya

Hukumar EFCC ta na tuhumar tsohon sakataren gwamnatin tarayyar da hannu a badakalar da ta shafi tsohuwar Ministar harkokin jirgin sama, Stella Oduah.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

2. Bola Tinubu

Hukumar CCT ta gurfanar da Bola Tinubu a kotu bisa zargin amfani da asusun bankunan waje a lokacin da yake gwamnan jihar Legas tsakanin 1999 da 2007.

A 2018 ne tsohon shugaban kamfanin Alpha Beta Consulting, Dapo Apara ya aikawa EFCC korafi, yana zargin Tinubu da laifin shan fadi da N100bn na haraji.

Tinubu, Saraki, Okorocha da Kalu
Masu harin 2023 da ake zargi da laifi
Asali: UGC

3. Bukola Saraki

A jerin da ICIR suka kawo, Bukola Saraki yana cikin masu neman mulkin da ba su sha ba. Ana zargin Saraki da satar kudi tun yana Darekta a bankin SGBN.

Tsakanin 2015 da 2021, tsohon shugaban majalisar dattawan ya yi ta kai-komo tsakanin EFCC, CCB da kotu a kan zargin satar kudi daga baitul malin jihar Kwara.

Kara karanta wannan

Jami'an tsaro sun kama mutane 28, sun kwato makamai da layoyi a jihar Neja

4. Dave Umahi

Wani da ake ganin yana neman shugabancin Najeriya shi ne gwamnan Ebonyi, David Umahi. ‘Yan kungiyar G-64 su na zargin gwamnatinsa da laifin cin wasu kudi.

‘Yan tafiyar G-64 su na tuhumar gwamnatin Umahi da batar da N6.7bn na kananan hukumomin.

5. Rochas Okorocha

Sanata Rochas Okorocha yana da bayanan da zai yi wa gwamnatin Imo a kan zargin wawurar kudin jama’a. Ana zargin ya bada kwangiloli na N20bn ba tare da ka’ida ba.

An kafa kwamiti ya binciki bashin kusan N112bn da aka samu ana bin gwamnatin jihar Imo a lokacinsa. Yanzu haka hukumar EFCC ta na binciken Sanatan na APC.

6. Orji Uzor Kalu

Shi kuwa Orji Uzor Kalu har gidan yari ya shiga bayan Alkali Mohammed Idris na babban kotun tarayya ya same shi da wasu laifuffukan da EFCC take zarginsa da su.

A 2020 kotun koli ta fito da tsohon gwamnan na Abia daga gidan gyaran hali, sannan wani Alkali ya haramtawa Lauyoyin EFCC yin shari’a da shi kan zargin cin kudi.

Kara karanta wannan

Yadda yunkurin zawarcin Jonathan, a ba shi takara a APC ya sha ruwa tun kafin a kai 2023

Asali: Legit.ng

Online view pixel