Alpha Beta: Babban Jigon PDP ya roki Jami’an EFCC su yi maza, su yi ram da Tinubu

Alpha Beta: Babban Jigon PDP ya roki Jami’an EFCC su yi maza, su yi ram da Tinubu

- Bode George ya yi kira ga hukumar EFCC ta binciki Asiwaju Bola Tinubu

- Jagoran adawar ya ce bai kamata irinsu Bola Tinubu suna neman mulki ba

- George ya ce ya tashi daga ‘Dan Najeriya idan Tinubu ya samu shugabanci

Bode George, daya daga cikin manyan kusoshin jam’iyyar PDP ya ce zai tashi daga ‘Dan Najeriya idan jagoran APC, Bola Tinubu ya zama shugaban kasa.

Da ya ke magana a gidan talabijin na Arise a ranar Juma’a, 7 ga watan Mayu, 2021, Bode George, ya yi kira ga hukumar EFCC ta cafke Asiwaju Bola Tinubu.

Cif Bode George ya na so a binciki rawar da kamfanin Alpha Beta Consulting ya taka a lokacin da Asiwaju Bola Tinubu yake rike da kujerar gwamnan Legas.

KU KARANTA: Ramadan: Tinubu ya dauki nauyin ciyar da mutum fiye da 4, 000 a Katsina

Ana zargin Asiwaju Bola Tinubu ne ya mallaki kamfanin karbar haraji na Alpha Beta Consulting.

Ya ce: “Na yi maganar nan a da, kuma zan sake fada a fili, EFCC ta yi maza ta binciki kamfanin Alpha Beta Consulting, wanda shi (Bola Tinubu) ya mallaka.”

“Bari in yi dalla-dalla, a wuri na raina hankali ne ace irinsa suna neman mulkin kasar nan.” Inji sa.

“Dole mu tabbatar an bincike shi. Ya na ta gararamba a ko ina – wannan raina hankalin masu hankali ne.”

KU KARANTA: An zabi Dr. Isa Pantami a matsayin Ministan da ya yi fice a 2021

Alpha Beta: Babban Jigon PDP ya roki Jami’an EFCC su yi maza, su yi ram da Tinubu
Bola Tinubu Hoto: premiumtimesng.com
Asali: UGC

“Idan aka yi haka ya zama shugaban kasa, na tashi daga matsayin ‘Dan Najeriya. Kuma ba wasa na ke yi ba.”

George ya yi magana a ka lamarin rashin tsaro, ya ce halin da ake ciki ya zama abin ban tausayi. ‘Dan siyasar ya yi kira ga malamai su ba matasa tarbiyya.

“Dole malamanmu su fito su yi magana, mu ba yaranmu tarbiyyar da ake bukata. Ina dabi’ar da mu ka koya a lokacin da mu ke kanana.” George ya tambaya.

A ranar Juma'a ne ku ka ji wasu Gwamnonin PDP sun yi zuga zuwa Kalaba, jihar Kuros-Riba da nufin hana Gwamna Ayade sauya-sheka zuwa jam'iyyar APC.

Gwamnonin sun lallabi Farfesa Ayade ya zauna a PDP. Gwamna Aminu Waziri Tambuwal da Ifeanyi Okowa da Ifeanyi Ugwuanyi su ka zauna da gwamnan.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng

Online view pixel