Da duminsa: EFCC ta damke tsohon gwamna, Rochas Okorocha, a Abuja

Da duminsa: EFCC ta damke tsohon gwamna, Rochas Okorocha, a Abuja

- Sanata Rochas Okorocha, tsohon gwamnan jihar Imo, ya shiga hannun hukumar yaki da rashawa da hana yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa

- Jami'an hukumar sun damke Okorocha ne a yammacin ranar Talata a garin Abuja bayan ya ki amsa gayyatar da suka dinga aiko masa da ita

- An gano cewa a halin yanzu yana hedkwatar hukumar inda yake amsa tambayoyi akan almundahanar wasu tarin kudade

Tsohon gwamnan jihar Imo, Rochas Okorocha, ya shiga hannun hukumar yaki da rashawa da hana yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa, jaridar Premium Times ta tabbatar.

Jami'an hukumar EFCC sun kama Okorocha wurin karfe 4 na yammacin Talata a ofishinsa dake Abuja, majiya ta tabbatar.

Majiyar da ta tabbatar, ta ce hukumar ta dinga tura gayyata ga tsohon gwamnan zuwa ofishinta dake Abuja saboda harkallar wasu kudade amma ya ki zuwa.

Okorocha, wanda yanzu sanata ne, ya ki zuwa gayyatar da aka yi masa, lamarin da ya fusata hukumar EFCC din kuma suka san hanyar kama shi.

KU KARANTA: Da duminsa: 'Yan ta'adda na shirin kaiwa filayen jiragen sama farmaki, FG

Da duminsa: EFCC ta damke tsohon gwamna, Rochas Okorocha, a Abuja
Da duminsa: EFCC ta damke tsohon gwamna, Rochas Okorocha, a Abuja. Hoto daga @Premiumtimes
Asali: Twitter

KU KARANTA: Fara azumin kafin sanarwan Sarkin Musulmi sabawa Manzon Allah ne, Ustaz Abu Jabir

A halin yanzu, hukumar EFCC na tuhumar dan siyasan a hedkwatarta kuma babu tabbacin ko za a bar shi ya tafi gida a yau din nan.

Bayanai a kan zargin da ake wa sanatan har a yanzu basu da yawa amma majiyoyi sun tabbatar da cewa suna da alaka da wasu kudade da suka bace yayin da yayi shekaru takwas a matsayin gwamnan Imo.

An kasa samun mai magana da yawun Okorocha, Sam Onwuemeodo, har a yammacin Talata kafin rubuta wannan rahoton.

A yayin da aka tuntubi mai magana da yawun EFCC, Wilson Uwujaren, ya tabbatar da cewa tsohon gwamnan yana hannun hukumar.

A wani labari na daban, lamari ya dauka zafi tsakanin wasu 'yan kwamitin rikon kwarya na majalisar wakila a kan makamai, da shugaban sojin kasa, Laftanal janar Ibrahim Attahiru bayan bincike a kan siyan makamai na sojin Najeriya.

Lamarin ya juya yayin da shugaban sojin kasan ya ki kara bayani kan wasu takardu da ya mika gaban kwamitin inda yace su duba takardun da kansu domin babu wani karin bayani.

Shugaban sojin ya jaddada cewa bai dade da hawa kujerarsa ba don haka ba shi ke da hakkin yin magana a kan makaman da magabatansa suka siya ba, Channels Tv ta wallafa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng