Abubuwan da su ka kai tsohon Gwamna Uzor Kalu gidan kurkuku

Abubuwan da su ka kai tsohon Gwamna Uzor Kalu gidan kurkuku

Bayan shekaru 12 ana ta faman shari’a, an samu tsohon gwamnan jihar Abia, Orji Uzor Kalu, da laifin satar dukiyar al’umma. An yanke wannan hukunci ne a Ranar 5 ga Watan Disamban 2019.

Legit.ng ta kawo wasu daga cikin dalilan da su ka sa babban kotun tarayya ta samu Sanatan na Abia ta Arewa da laifuffukan da hukumar EFCC mai yaki da barayin kasa ta ke tuhumarsa da su.

Ga jerin manyan kura-kuran da Orji Uzor Kalu ya yi:

1. Gauraya shagulolin Iyali da sha’anin Gwamnati

Daya daga cikin kura-kuren da Orji Kalu ya yi shi ne amfani da wani kamfanin danginsa mai suna Slok Nigeria LTD a wajen harkokin gwamnatin jihar Abia. An samu tsohon gwamnan da laifin karkatar da biliyan 7.65 na jihar Abia da sunan wannan kamfani tsakanin 1999 zuwa 2007.

KU KARANTA: Kalu ya roki Jami'ai su guji maka masa mari a hannu

2. Tsoma hannu a cikin Baitul-Mali

EFCC mai yaki da masu yi wa tattalin arzikin Najeriya zagon-kasa ta zargi tsohon gwamna Uzor Kalu da tsohon Ma’aikacin kudi na jihar Abia, Udeh Udeogu, da yin gaba da miliyan 460 daga asusun gwamnati. Wannan ya na cikin gangancin da Sanatan ya yi a kan karagar mulki.

3. Dawowa APC daga PDP babu nauyi

A matsayinsa na daya daga cikin kusoshin da su ka kafa jam’iyyar PDP a Kudu maso Gabashin Najeriya, Uzor Kalu ya tsere daga PDP zuwa APC ba tare da an yi wata yarjejeniya mai karfi ba. Ana tunanin cewa da a ce Kalu ya samu wata yarjejeniya kafin dawowa APC, da ba haka ba.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit.ng

Online view pixel