Matasan Arewa sun zabi Ministan Buhari ya zama Magajinsa a 2023, sun kawo dalilai 5

Matasan Arewa sun zabi Ministan Buhari ya zama Magajinsa a 2023, sun kawo dalilai 5

  • Coalition of Northern Youth for Good Governance ta ce mulkin Najeriya a 2023 sai Rotimi Amaechi
  • Kungiyar matasan Arewa mai son shugabanci nagari ta ce Ministan sufurin ya dace da shugaban kasa
  • Shugaban CNYGG, Bilal Dakiyak ya ce Amaechi bai tsufa ba, ya san kan-aiki, kuma Buhari ya kawo shi

Abuja - Gamayyar kungiyar Coalition of Northern Youth for Good Governance (CNYGG) sun yi wa Ministan sufuri na tarayya, Rotimi Amaechi mubaya’a.

Jaridar The Guardian ta fitar da rahoto cewa kungiyar CNYGG ta na goyon bayan Rotimi Amaechi ya zama shugaban Najeriya bayan Muhammadu Buhari.

A cewar wannan kungiya ta matasan Arewa, babu wanda ya fi dacewa ya cigaba da jagorancin al’umma kamar yadda aka dauko aiki irin Rotimi Amaechi.

Rahoton ya ce kungiyar ta bayyana wannan ne a lokacin da ta kira wani taron zantawa da manema labarai jiya, 31 ga watan Junairu 2022, a garin Abuja.

Kara karanta wannan

Tinubu ne zai ci: Malamin addini ya yi hasashen zaben 2023

Shugaban tafiyar CNYGG na kasa, Kwamred Bilal Dakiyak ya bayyana cewa ko ta ina aka je aka dawo, Amaechi ya cancanta da ya tsaya takarar shugaban kasa.

Minista da Buhari
Rotimi Amaechi tare da Muhammadu Buhari Hoto: Twitter
Asali: Twitter

Meyasa CNYGG ta zabi Amaechi?

The Nation ta rahoto Kwamred Dakiyak yana mai cewa Ministan ya wuce a kira sa yaro, sannan kuma bai yi tsufar da zai rika fama da larurar rashin lafiya ba.

Kwamred Bilal Dakiyak ya ce Amaechi ya san kan aiki tun da ya rike kujerun majalisar dokoki na jiha da gwamna kafin ya zama Minista a majalisar zartarwa.

Bugu da kari, kungiyar ta na ganin Ministan sufurin ya san matsalolin da ke addabar Najeriya, kuma a matsayinsa na wanda Buhari ya dauko, ya san mafita.

Kamar yadda ku ka sani, har yau Amaechi mai shekara 56 a Duniya bai ce zai yi takara a 2023 ba.

Kara karanta wannan

Kisan gillan Hanifa: Ministan ilimi ya yabawa kokarin da gwamnatin Kano ke yi

Duk da haka Dakiyak ya yi kira ga tsohon gwamnan na Ribas ya nemi tikiti a APC domin ya na da mutane ko ina a Najeriya, kuma ya yi abin a yaba a kujerar Minista.

Zan iya goyon bayan Saraki - Clark

An ji cewa tsohon Minista a zamanin Janar Yakubu Gowon, Edwin Kiagbodo Clark mai shekara 94 ya karbi maganar takarar Bukola Saraki da hannu biyu-biyu.

Tsohon shugaban majalisar dattawa, Saraki ya fara yakin neman tikitin takarar shugaban kasa, kuma Clark ya ce zai iya mara masa baya amma da sharadi daya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel