Ado Doguwa ya samu karuwar 'diya na 28, ya lashi takobin haifan 30 kafin 2023

Ado Doguwa ya samu karuwar 'diya na 28, ya lashi takobin haifan 30 kafin 2023

Allah ya azurta Shugaban masu rinjayen majalisar wakilan tarayya, Alhassan Ado Doguwa, da karuwar 'da na ashirin da takwas (28) daga daya daga cikin matansa hudu.

Ado Doguwa ya bayyana hakan ranar Talata a zauren majalisa yayinda takwaransa, Hanrabul Ndudi Elumelu, ya taya sa murna, rahoton Tribune.

Dan majalisan ya yi alkawarin cewa ba zai daina hayayyafa ba saboda har yanzu da sauran karfinsa kuma zai haifi 30 kafin zaben 2023.

Ya lashi takobin haifan 30 kafin 2023
Ado Doguwa ya samu karuwar 'diya na 28, ya lashi takobin haifan 30 kafin 2023 Hoto: HouseNGR
Asali: UGC

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A cewarsa:

"Da gaske ne na samu karuwar 'diya. Mace ce. Mahaifiyar da diyar na cikin koshin lafiya. Mijin kuwa har yanzu yana nan daram dam. Ina godewa Allah cewa na cika alkawarin da na yiwa gidan nan cewa zan cigaba da hayayyafa. Insha Allahu zan cigaba."

Kara karanta wannan

Shugaba a 2023: Fulani sun yi watsi da 'yan takara daga Arewa, sun fadi zabinsu

"Ina kira ga mambobi suyi watsi da dokokin majalisa su samar da sabuwar dokar cewa duk mai 'yaya 30 a bude masa rumfar zabe a gidansa."

Kakakin majalisa kuwa, Femi Gbajabiamila ya taya shi murna.

Asali: Legit.ng

Online view pixel