Najeriya ce ta 1 cikin jerin kasashen Afrika da ake amfani da man Bilicin, Sabon Bincike

Najeriya ce ta 1 cikin jerin kasashen Afrika da ake amfani da man Bilicin, Sabon Bincike

Matan Najeriya sun ciri tuta a sabon rahoton adadin masu amfani da man canza launin fata watau man bilicin.

Binciken da CNN ta gudanar ya nuna cewa Najeriya ce ta daya cikin jerin kasashen nahiyar Afrika da ake amfani da man sauya launin fata.

Rahoton binciken ya yi bayanin cewa kashi 75% na matan Najeriya na sayan man bilicin.

Daga Najeriya sai kasar Senegal masu 60%, Mali masu 50% da kuma Ghana masu mata 30%.

Wadannan kayan shafe-shafe na da sinadarai dake rage samuwar garkuwan jikin bakin mutum watau Melanin.

Masana ilmin fata da dama sun bayyana illan amfani da wadannan kayan shafe-shafe ga lafiyar jikin mutum.

Kara karanta wannan

Labari mai dadi: Sojoji sun gano wata kasuwa da mafakar ISWAP, sun kone su kurmus

Sabon Bincike
Najeriya ce ta 1 cikin jerin kasashen Afrika da ake amfani da man Bilicin, Sabon Bincike
Asali: Instagram

Asali: Legit.ng

Online view pixel