2023: Ƙungiyar Arewa Ta Buƙaci Tsohon Gwamnan Bauchi, Mu’azu, Ya Fito Takarar Shugaban Ƙasa

2023: Ƙungiyar Arewa Ta Buƙaci Tsohon Gwamnan Bauchi, Mu’azu, Ya Fito Takarar Shugaban Ƙasa

  • Kungiyar matasan Arewa ta North-East Young Technocrats For Good Governance ta yi kira ga tsohon gwamnan Bauchi, Adamu Mu'azu ya fito takara a 2023
  • Kungiyar ta bayyana cewa tsohon shugaban na PDP na kasa yana da kwarewa da iya aiki yasa ya cancanci dare wa kujerar shugaban kasar a 2023
  • Ta kuma bayyana cewa duba da irin ayyukan da ya yi a baya, zai iya hada kan kasa sannan ya habbaka tattalin arziki ya samar da tsaro da wasu ababen da ake bukata a kasa

Gamayyar matasa karkashin kungiyar North-East Young Technocrats For Good Governance ta yi kira ga tsohon gwamnan Jihar Bauchi kuma tsohon shugaban jam'iyyar PDP na kasa, Ahmadu Adamu Mu'azu, ya fito takarar shugaban kasa a 2023.

Shugaban kungiyar na kasa, Dr Mohammed Abdullahi da Sakatare, Mr Solomon David cikin wata takarda da suka fitar a Bauchi sun ce tsohon gwamnan yana da gaskiya da rikon amana da zai iya yakar rashawa da rashin adalci a kasar, Vanguard ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Zaben 2023: Dan Shehu Dahiru Bauchi ya fito takarar shugaban kasa na 2023

2023: Ƙungiyar Arewa Ta Buƙaci Tsohon Gwamnan Bauchi, Mu’azu, Ya Fito Takarar Shugaban Ƙasa
'Kungiyar Arewa Ta Buƙaci Tsohon Gwamnan Bauchi, Adamu Mu’azu, Ya Fito Takarar Shugaban Ƙasa a 2023. Hoto: Vanguard
Asali: Facebook

A cikin takardar, sun ce Mu'azu zai magance wariya, rashin tsaro, talauci, kabilanci da sauran abubuwan yau da kullum da ke adabar kasar.

Adamu Mu'azu ya sa aiki ga kwarewa da zai iya hada kan Najeriya ya ceto ta a 2023

Kungiyar ta kuma ce tsohon gwamnan na Jihar Bauchi, da kwarewarsa da iya aiki zai iya hada kan kasa sannan ya habbaka tattalin arziki kamar yadda ya zo a rahoton na Vanguard.

Kungiyar ta ce:

"Allah ya albarkaci Najeriya da hazikan maza da mata masu halaye na gari kamar Ahmadu Mu'azu, mutum mai karamci wanda shine tsohon shugaban jam'iyyar Peoples Democratic Party PDP na kasa. Mun yi imanin ya cancanci ya jagoranci kasar nan idan aka bashi hadin kai da ya ke bukata daga masu ruwa da tsaki.

Kara karanta wannan

Mai shari'a ta caccaki DSS, ta ce ka da su kara kawo Nnamdi Kanu gaban kotu da kaya daya

"Ya cancanci ofishin shugaban kasa a wannan lokaci da ake bukatar wanda zai hada kan kasa. Zai iya hada kawo cigaba da farantawa yan kasa rai baki daya.
"Don haka, duba da niyyar mu na ganin an gina kasa, ya kamata a bawa adalin mutum kamar Ahmadu Mu'azu dama duba da ayyukan da ya yi a baya. Ku zo mu yi tafiya ta gina kasa a 2023 ta hanyar bawa jajirtaccen mutum dama."

Kungiyar ta kara da cewa duk inda ya yi aiki, ya nuna jajircewarsa da bajinta musamman wurin kawo cigaba a Jihar Bauchi lokacin da ya yi gwamna shekaru takwas. Har yau ayyukansa ne suka sa jihar ta yi fice.

2023: Manya masu son satar dukiyar talakawa ne ba su son a sake samun wani Buharin, Garba Shehu

A wani labarin daban, Fadar Shugaban Kasa ta ce manyan mutane masu aikata rashawa ne ba su son a sake samun 'wani Buhari' a Najeriya saboda wata manufarsu na gina kansu, Daily Trust ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Shugaban kasa a 2023: Shugaban PDP ya yi magana kan magajin Buhari

Mai magana da yawun Shugaba Muhammadu Buhari, Garba Shehu, cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Talata, ya ce zai yi wahala a samu wani shugaba da zai iya zarce irin ayyukan da Buhari ya yi.

Ya yi bayanin kan dalilin da yasa Buhari ba zai 'bari a cigaba da yadda ake harka' a kasar ba a karkashin gwamnatinsa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164