Zaben Anambra: Wa'adin shigar da kara ya kusa karewa, APC ba ta shigar da kara ba
- Kwanaki kadan suka rage wa'adin shigar da karar kalubalantar zaben gwamna a jihar Anambra amma shuru babu wanda ya shigar da kara
- Wannan batu na zuwa ne yayin da wa'adin ya rage saura kwanaki shida kacal daga cikin 21 da aka bayar da shigar da kara kan zaben
- A bangaren 'yan APC, sun bayyana cewa, suna nan kan bakarsu cewa, basu amince sun fadi a zaben da aka gudanar ba
Anambra - Daily Trust ta ruwaito cewa, saura kwanaki shida a cika wa’adin gabatar da kara domin kalubalantar sakamakon zaben gwamnan jihar Anambra, kotun sauraron kararrakin zabe ta jihar ba ta karbi batun ba daga wata jam'iyya ba har yanzu.
A cewar dokar, ‘yan takara da jam’iyyunsu da suka sha kaye suna da hurumin kwanaki 21 daga ranar da hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC ta sanar da zabe domin su gabatar da kara.
A ranar 10 ga watan Nuwamba ne jami’ar kula da zabe na jihar Anambra, Farfesa Florence Obi, ta ayyana Farfesa Charles Soludo na jam’iyyar APGA a matsayin wanda ya lashe zaben.
Bayan kwanaki uku, dan takarar jam’iyyar APC a zaben, Sanata Andy Uba, da dan takarar jam’iyyar ADP, Mista Afam Umezeoke, sun nuna sha’awarsu na kalubalantar sakamakon zaben a kotu, inji rahoton Daily Trust.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Sai dai, sakataren kotun, Barr. Surajo Gusau, ya ce kotun ba ta karbi koke daga wata jam’iyya ko dan takara ba.
Ya ce an kafa kwamitin ne nan take bayan bayyana sakamakon zaben jihar.
A cewarsa, a matsayinsa na sakataren kwamitin, ya amsa kiran kwamitin kwana guda bayan bayyana sakamakon zaben, wanda ya nuna cewa an kafa kwamitin.
Dangane da fargabar da ake yi a wasu bangarori na cewa kwamitin na iya zama a Abuja maimakon Awka saboda rashin tsaro, ya ce za a iya hakan ne kawai idan an samu wasika a hukumance zuwa ga shugaban kotun daukaka kara, Hon. Justice Dongban Mensam.
Ya yi watsi da rahoton cewa da zarar an gabatar da koke ko ma wani kudiri game da zaben, to tabbas kwamitin zai zo Awka.
Mai ba Umezeoke da mataimakin shugaban jam’iyyar Kudu maso Gabas na kasa Barr. Emeka Agbapuonwu shawara, wanda ya zanta da manema labarai a Awka ranar Talata ya ce har yanzu akwai sauran lokacin da za su gabatar da kara.
A cewarsa, shi da dan takararsa sun kammala dukkan shirye-shiryen mika kokensu kuma za su cika wa’adin.
Haka kuma wani jigo a jam’iyyar APC kuma memba a Andy Uba Campaign Organisation, Prince Bounty Onuigbo, ya bayyana cewa babu wani abin tsoro, yana mai cewa tabbas dan takarar nasa zai yi komai kafin wa'adin..
Mai ba Gwamna Willie Obiano shawara na musamman kan harkokin siyasa Bar Ifeatu Obiokoye, ya ce jam’iyyarsu a shirye take ta fuskanci duk wani mai shigar da kara a gaban kotu, inda ya kara da cewa Soludo ba a kwance kawai yake ba.
2023: Masu neman takarar gwamna 7 daga APC da PDP na shirin sauya sheka zuwa APGA a wata jihar kudu maso gabas
Ya kuma kara da cewa, a yayin da ake jiran kara daga Uba da jam’iyyar APC, kada mutane su manta da wata kara da aka shirya domin yanke hukunci na kalubalantar takarar jam’iyyar APC wanda daya daga cikin ‘yan takararta Cif George Muoghalu ya shigar.
Ni fa ban yarda na fadi zabe ba, zamu hadu a kotu - Andy Uba na APC
A baya kunji cewa, dan takaran jam'iyyar All Progressives Congress (APC) a zaben gwamnan Anambra da aka kammala, Andy Uba, yace sam ba yarda da sakamakon zaben da INEC ta sanar ba.
A cewarsa, ta yaya zai fadi a zabe a gundumomin da shugabannin APGA suka koma APC ana saura mako daya zabe.
Andy Uba ya bayyana haka ne ranar Asabar yayinda jawabi ga mambobin jam'iyyar APC, rahoton DailyTrust.
Asali: Legit.ng