Siyasar Kano: Jiga-jigan APC 10 da suka kai karar Gwamna Ganduje wajen uwar Jam’iyya

Siyasar Kano: Jiga-jigan APC 10 da suka kai karar Gwamna Ganduje wajen uwar Jam’iyya

  • Wasu jagororin jam’iyyar APC na reshen Kano sun yi zama da Mai Mala Buni
  • ‘Yan jam’iyyar sun ja daga ne a karkashin Sanata na tsakiya, Ibrahim Shekarau
  • Sauran ‘yan tawaren sun kunshi irinsu Barau Maliya, Sharada da Tijjani Jobe

Abuja - A ranar Laraba, 13 ga watan Oktoba, 2021, wasu jagororin jam’iyyar APC na Kano, suka hadu a gidan tsohon gwamna Malam Ibrahim Shekarau.

Ibrahim Shekarau wanda Sanata ne mai wakiltar yankin Kano ta tsakiya a majalisar dattawa, ya jagoranci wadannan kusoshi har zuwa hedikwatar APC.

Mun tattaro jerin ‘yan siyasan Kano da suka kai korafin gwamnatin jiha gaban uwar jam’iyya kamar yadda Sha'aban I. Sharada ya bayyana Facebook:

1. Ibrahim Shekarau

Ibrahim Shekarau shine ‘dan siyasa na farko da ya fara zarce wa a kan kujerar gwamnan Kano. Sanatan ya yi takarar shugaban kasa a zaben 2011. A 2014 ya zama Ministan ilmi.

Kara karanta wannan

Allah ya yi wa matar Marigayi Sheikh Abubakar Gumi rasuwa

2. Barau Ibrahim Jibrin

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Sanata Barau I Jibrin shi ne mai wakiltar Kano ta Arewa a majalisar dattawa tun 2015. Barau ya taba wakiltar yankin Tarauni a majalisar wakalai, ya rike mukamai a gwamnatin jihar Kano.

3. Hon. Tijjani Abdulkadir Jobe

Hon. Tijjani Abdulkadir Jobe ‘dan kasuwa ne wanda yanzu yake wakiltar mazabar Dawakin-Tofa, Tofa da Rimin Gado a majalisar wakilan tarayya, yankin Gwamna Abdullahi Ganduje.

A 2007 aka fara zaben Jobe a matsayin ‘dan majalisa, ya sake lashe zabe a 2011, 2015 da 2019.

Siyasar Kano
Wasikar 'Yan taware Hoto: Shaaban Sharada
Asali: Facebook

4. Hon. Nasiru Abduwa Gabasawa

Nasiru Abduwa Gabasawa shi ne ‘dan majalisar mutanen Gezawa da Gabasawa. Hon. Gabasawa ya dade a siyasa, ya taba zama shugaban karamar hukuma a 1990 da sakataren SDP a 1989.

5. Hon. Haruna I. Dederi

‘Dan majalisar mai wakiltar yankin Karaye da Rogo a majalisar wakilai yana cikin ‘yan tawaren da suka yi zama a Abuja. Haruna Dederi yana cikin manyan APC a yankin Kano ta kudu.

Kara karanta wannan

Ana kishin-kishin wani gagarumin sauya sheka yayin da shugaban APC ya gana da shahararren gwamnan PDP

6. Sha’aba Sharada

Hon. Sha'aban Ibrahim Sharada matashin ‘dan jarida ne da ya koma siyasa. Kafin zaman sa ‘dan majalisar Birni da kewaye, yana cikin masu ba shugaba Muhammadu Buhari shawara.

7. Shehu Dalhatu

Alhaji Shehu Dalhatu wanda shi ne shugaban kungiyarBuhari Support Organisation (BSO) na reshen jihar Kano ya na cikin tawagar Malam Ibrahim Shekarau da ta kai korafi a Abuja.

8. Muazu Magaji

Injiniya Muazu Magaji ya na cikin ‘yan Rescue Kano Coalition. Tsohon kwamishinan ayyukan na Kano ya halarci zaman da aka yi bayan ya dawo daga ziyarar ta’aziyya a garin Yola, Adamawa.

9. Alhaji Ahmadu Haruna Danzago

Ahmadu Haruna Danzago yana cikin tafiyar tawaren. Danzago yana cikin masu yakar Abdullahi Abbas wajen zama shugaban APC na jiha. Kafin yanzu ya yi shugaban CPC a Kano.

10. Kabiru Gaya

Kabiru Ibrahim Gaya mai wakiltar Kano ta kudu a majalisar dattawa yana cikin wadanda aka fara zaman da su. Amma daga baya ya janye kansa, bai cikin wadanda suka sa hannunsu.

Kara karanta wannan

Rikicin APC: Shekarau ya bayyana makasudin kai korafin Ganduje gaban Shugabannin APC na kasa

Jiga-jigan APC
Wasikar 'Yan tawaren na APC a Kano Hoto: Shaaban Sharada
Asali: Facebook

Asali: Legit.ng

Online view pixel