Jam'iyya Zata Maka Tinubu a Kotu Kan Bayanan Bogi a Takardun Karatunsa

Jam'iyya Zata Maka Tinubu a Kotu Kan Bayanan Bogi a Takardun Karatunsa

  • Jam’iyyar Action Peoples Party (APP) ta bayyana cewa tana shirin maka Bola Ahmed Tinubu, 'dan takarar shugabancin kasa na APC a gaban kotu
  • Shugaban APP na kasa, Uche Nnadi yace za su kalubalanci kan bayann bogi da ya mika wa INEC kan batun karatunsa a 2007 yanzu ya kuma mika mabanbanta
  • Ya sanar da cewa, a baya Tinubu yace yana da digiri har biyu daga jami'ar Chicago amma yanzu ya sanar da cewa bai yi makarantun firamare da sakandare ba

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Jam’iyyar Action Peoples Party (APP) na shirin maka dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar All Progressives Congress (APC), Bola Ahmed Tinubu a gaban kotu don kalubalantar kwalin karatunsa.

Matakin ya biyo bayan zargin wasu kura-kurai a takardun karatun da Tinubu ya gabatarwa hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta (INEC), Jaridar Leadership ta ruwaito

Kara karanta wannan

Jerin zargin rashin gaskiya da ke jikin ‘Yan takaran 2023, Atiku Abubakar da Bola Tinubu

Jam'iyya Zata Maka Tinubu a Kotu Kan Bayanan Bogi a Takardun Karatunsa
Jam'iyya Zata Maka Tinubu a Kotu Kan Bayanan Bogi a Takardun Karatunsa. Hoto daga leadership.ng
Asali: UGC

Shugaban jam’iyyar ta APP, Uche Nnadi, ne ya bayyana hakan a ranar Juma’a, 24 ga watan Yuni, yana mai cewa jam’iyyar na da isassun hujojji a kan haka.

A cewar Nnadi, jerin sunayen yan takara da INEC ta saki ya nuna Tinubu bai cancanci yin takara ba domin takardunsa na kunshe da bayanan karya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya ce:

“Tinubu ya musanta batun zuwa makarantun firamare da sakandare amma ya yi ikirarin mallakar digiri a sabbin takardun da INEC ta wallafa a yau.
“Tinubu ya yi rantsuwar karyar ne yayin da ya yi watsi da ikirarinsa na farko na halartan makarantar sakandare, ya yi rantsuwar ne don takarar gwamna amma a yanzu yana ikirarin bai yi makarantar firamare ba. Sabuwar takardar ta Tinubu ya ci karo da rantsuwar da ya yi a 2007 cewa ya halarci makarantun firamare da sakandare.”

Kara karanta wannan

Musulmi da Musulmi: Zanga-zanga ta barke a sakateriyar APC saboda adawa da zabin Tinubu

Ekiti 2022: Abubuwa sun fara yi wa jam'iyyar APC kyau, Shugaba Buhari

A wani labari na daban, Shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, ya bayyana nasarar da Biodun Oyebanji, ya samu a zaɓen gwamnan jihar Ekiti a matsayin wata alama da ke nuna abubuwa na gyaruwa a APC.

Oyebanji, tsohon Sakataren gwamnatin Ekiti, ya samu nasara ne da kuri'u 187,057, inda ya lallasa manyan yan takarar da ke biye masa a baya na jam'iyyar SDP da PDP, kamar yadda Punch ta ruwaito.

Zababben gwamnan tare da rakiyar shugaban APC, gwamna Kyode Fayemi, , gwamna Badaru Abubakar da wasu gwamnoni sun ziyarci shugaba Buhari a Aso Villa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel