Ekiti 2022: Abubuwa sun fara yi wa jam'iyyar APC kyau, Shugaba Buhari

Ekiti 2022: Abubuwa sun fara yi wa jam'iyyar APC kyau, Shugaba Buhari

  • Shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, ya nuna tsantsar farin cikinsa da nasarar APC a zaɓen gwamnan jihar Ekiti
  • Buhari ya ce nasarar Oyebanji a zaɓen ranar Asabar wata babbar alama ce da ke nuna APC ta dawo kan hanya, abubuwa sun fara kyau
  • Oyebanji tare da rakiyar kusoshin APC na ƙasa ya ziyarci shugaban ƙasa a fadarsa da ke birnin tarayya Abuja ranar Litinin

Abuja -Shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, ya bayyana nasarar da Biodun Oyebanji, ya samu a zaɓen gwamnan jihar Ekiti a matsayin wata alama da ke nuna abubuwa na gyaruwa a APC.

Oyebanji, tsohon Sakataren gwamnatin Ekiti, ya samu nasara ne da kuri'u 187,057, inda ya lallasa manyan yan takarar da ke biye masa a baya na jam'iyyar SDP da PDP, kamar yadda Punch ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Sabuwar matsala ta kunno wa Atiku da Tinubu, Dubbannin mambobin APC, PDP sun canza ɗan takarar da zasu zaɓa a 2023

Shugaba Buharida tawagar zaɓabɓen gwamnan Ekiti.
Ekiti 2022: Abubuwa sun fara yi wa jam'iyyar APC kyau, Shugaba Buhari Hoto: Buhari Sallau/facebook
Asali: Facebook

Zababben gwamnan tare da rakiyar shugaban APC, gwamna Kyode Fayemi, , gwamna Badaru Abubakar da wasu gwamnoni sun ziyarci shugaba Buhari a Aso Villa.

A wata sanarwa da Hadimin shugaban ƙasa, Femi Adesina, ya fitar, shugaba Buhari ya yaba da ɗumbin goyon bayan da gwamnoni suka bai wa ɗan takarar na APC.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Premium Times ta ruwaito Buhari ya ce:

"Na ji daɗi kuma na ƙaunaci yadda gwamnoni suka haɗa kan su baki ɗaya suka nuna maka goyon baya."
"Ina tunanin jam'iyyr mu na da sa'a kuma abubuwa sun fara gyaruwa a jam'iyyar APC. Ina taya shugaban jam'iyya murna tare da fatan ku ɗore a haka."

A cikin sanarwan, shugaban ƙasan ya ce ya bibiyi yadda zaɓen ya gudana ranar Asabar 18 ga watan Mayu kuma ya gamsu da yadda masu zaɓe da jami'an tsaro suka ba da haɗin kai wajen tafiyar zaɓen.

Kara karanta wannan

Muhimman abubuwa 5 da ya kamata ku sani game da sabon gwamnan Ekiti

Shugaban APC, Sanata Abdullahi Adamu, ya miƙa baki ɗaya nasarar ga Allah mai girma da ɗaukaka, ya kuma lashi takobin ganin haka ta faru a jihar Osun wata mai zuwa.

Dole mu yaba wa Buhari - Gwamna Badaru

A ɓangarensa shugaban kwamitin yaƙin neman zaɓen gwamnan Ekiti, Gwamna Badaru na Jigawa, ya taya shugaba Buhari murnar cin nasara a wannan tafiyar da cewa:

"Goyon bayanka gagara misali wajen gyara jam'iyya ya fara haifar da ɗa mai ido. Idan ma aka haɗa kuri'un yan takarar da suka zo na biyu da na uku duk da haka na APC ya lallasa su da tsereya mai nisa."

A wani labarin na daban kuma Kotu ta dakatar da INEC daga rufe rijistar katin zaɓe a Najeriya

Babbar Kotun tarayya da ke zamanta a birnin tarayya Abuja ta dakatar da hukumar zaɓe mai zaman kanta INEC daga rufe rijistar Katin Zaɓe a ranar 30 ga watan Yuni, 2022.

Kara karanta wannan

2023: 'Ka ci amanar mu' Gwamna Okowa da Atiku ya zaɓa mataimaki ya shiga tsaka mai wuya

The Cable ta ruwaito cewa hukumar INEC ta zaɓi ranar 30 ga watan Yuni a matsayin ranar da zata rufe damar yin Katin zaɓe (CVR) yayin da take shirye-shiryen tunkarar babban zaben 2023.

Asali: Legit.ng

Online view pixel