Wani babban jigon jam'iyyar APC ya sauya sheka zuwa jam'iyyar PDP

Wani babban jigon jam'iyyar APC ya sauya sheka zuwa jam'iyyar PDP

  • Jam'iyyar PDP mai mulkin jihar Akwa Ibom ta yi babban kamu na jigon APC a jihar
  • Ɗan uwa ga sakataren kwamitin rikon kwarya na APC ta ƙasa ya sauya sheƙa zuwa PDP a Akwa Ibom
  • Yace ya ɗauki wannan matakin ne bayan gano cewa PDP ce ta dace da muradin al'ummar jihar Akwa Ibom

Akwa Ibom - Jam'iyyar APC ta kama hanyar rushewa a jihar Akwa Ibom, yayin da babban jigonta kuma ɗan uwa ga sakatare na ƙasa ya koma PDP, kamar yadda Vanguard ta ruwaito.

Da yake bayyana sauya shekarsa a ofishin shugaban PDP na jiha, Godwin Udoedehe, yace jam'iyyar PDP ce kaɗai kudurorinta da aikinta ya dace da muradin mutanen jihar Akwa Ibom.

PDP da APC
Wani babban jigon jam'iyyar APC ya sauya sheka zuwa jam'iyyar PDP Hoto: dailypost.ng
Asali: UGC

A jawabinsa yace:

"Maganar gaskiya shine, ba wai sa'a bace kaɗai yasa mutane suka zaɓi jam'iyyar PDP a matsayin jam'iyyar siyasar da tafi kwanta musu a rai tun bayan dawowar demokaraɗiyya a 1999."

Kara karanta wannan

Yanzu-yanzu: Yan Majalisar Wakilai sun amince da Kasafin Kudin 2022, sun kara N700bn

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Wannan ta faru ne saboda PDP ba ta gaza ba wajen kwatanta aiwatar da ayyukan da zasu kawo wa mutanen jihar cigaba."
"Idan ka duba jihohin da APC ke mulki zaka ga irin gurbata abubuwa da ta yi.Dan haka a wuri na sake dawo wa PDP na nuna kauna ta da cigaban jihr Akwa Ibom."

Maraba da dawo wa gida - PDP

Da yake jawabin karban mai sauya shekan, shugaban PDP na jihar, Hon Elder Aniekan Akpan, ya yaba wa Udoedeghe bisa ɗaukar matakin dawo wa gida.

Ya kuma ƙara da cewa jam'iyyar PDP a shirye take ta ba shi wurin zama kuma ta yi aiki tare da shi.

Yace:

"Inuwar jam'iyyar PDP tana da girman da zata ɗauki duk wani ɗan jihar Akwai Ibom dake son shigowa cikinta."
"Dan haka muna kira ga duk wani ɗan uwa ko yar uwa ga guguwar siyasa ta ɗibe shi zuwa wata jam'iyyar siyasa kuma yake sha'awar dawowa gida, to ya dawo."

Kara karanta wannan

Rikicin jam'iyyar APC a jihar Kano ba zai raba mun hankali ba, Gwamna Ganduje

A wani labarin kuma Manyan jiga-jigan PDP da daruruwan mambobi sun sauya sheka zuwa jam'iyyar APC mai mulki

Jiga-jigan PDP tare da dandazon magoya bayansu daga mazaɓar sanata ta kudancin jihar Cross Ribas sun sauya sheka zuwa jam'iyyar APC ranar Alhamis.

Gwamnan jihar Ben Ayade, yace babu kowa a jam'iyyar PDP ta jihar, tsagin adawa ya mutu murus.

Asali: Legit.ng

Online view pixel