Mai Wushirya: Bayan Tsawon Lokaci Yana Bidiyon Fitsara da Wadarsa, Kotu Ta Dauki Mataki
- Kotun majistare ta Kano ta tura ɗan TikTok mai suna Ashiru Idris da ake yi wa lakabi da Mai Wushirya gidan gyaran hali
- An kama shi ne bayan ya shafe tsawon lokaci yana dauka da yada bidiyon fitsara da wata wada da ya ke kira 'Yar Gudaliya
- Daga cikin irin bidiyon da ya ke yada wa akwai inda ya ke daga 'Yar Gudaliya da sumbatar kumatunta da sunan bidiyon bikin aurensu
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kano – Kotun majistare mai lamba 7 da ke Kano ƙarƙashin Mai Shari’a Halima Wali ta bayar da umarni a kan fitaccen 'dan TikTok, Ashiru Idris.
Idris, wanda aka fi sani da Mai Wushirya ya fara daukar hankali bayan sabon salon dora bidiyo da ya ke yi a shafukansa na sada zumunta, musamman Tiktok.

Source: Facebook
Labarin da Legit ta samu ya tabbatar da cewa cewa kotun ya aika da Mai Wushirya gidan gyaran hali na tsawon makonni biyu kafin ci gaba da sauraron shari’arsa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kotu ta tura 'dan TikTok zuwa kurkuku
Jaridar 21st Century ChronicleRahoton ya kara da cewa jami’an Hukumar Tace Fina-finai ta Jihar Kano ne suka kama shi makon da ya gabata.
An kama shi ne bayan wani bidiyo ya bazu a shafukan sada zumunta, inda aka ganshi ba riga tare da aikata abin da hukumomi suka kira “aikata mummunan ɗabi’a da ƙazanta” da 'Yar Gudaliya.
Hukumar tace fina-finai ta bayyana cewa irin waɗannan bidiyoyi na ɓata tarbiyya, sun kuma saɓa wa dokokin tace fina-finai na jihar.
Hukumar ta ce dokokinta sun haramta yaɗa bidiyon batsa wanda ke ƙunshe da abubuwan da ke da nuni da lalata da kuma bata tarbiyya.
Kotu na neman 'Yar Tiktok, 'Yar Gudaliya
Da yake magana da manema labarai bayan zaman kotu, Jami’in hulɗa da jama’a na hukumar, Abdullahi Sani Sulaiman, ya bayyana cewa kotu ta nemi a zo da 'Yar Gudaliya a zama na gaba.
Ya ce:
"Kotun ta bayar da umarnin a kawo abokiyar aikinsa gaban kotu kafin ci gaba da shari’a. Kafin mu gurfanar da shi, mun yi ƙoƙari ya taimaka mana wajen gano inda take, amma ya ƙi. Yanzu da kotu ta bayar da umarni, muna da tabbacin za mu samu nasarar kawo ta."

Source: Facebook
Ya ƙara da cewa hukumar ta samu rahoton cewa matar ta tsere zuwa jihar Zamfara, amma ana ci gaba da ƙoƙarin dawo da ita zuwa Kano domin fuskantar shari’a tare da Mai Wushirya.
Abdullahi ya ce:
“Ba za mu gaza ba har sai an dawo da ita don ta fuskanci hukunci kamar yadda doka ta tanada.”
Rahotanni sun nuna cewa shari’ar za ta ci gaba da gudana bayan cikar makonni biyu da kotu ta bayar da umarnin tsare ɗan TikTok ɗin a gidan gyaran hali.
Kotu ta aika 'dan TikTok kurkuku
A baya, mun wallafa cewa fitaccen ɗan TikTok daga jihar Kano, Abubakar Ibrahim, wanda aka fi sani da G-Fresh, ya sake shiga hannun hukuma saboda zargin wulakanta takardar Naira.
Wannan karo, kotun tarayya da ke Kano ta yanke masa hukuncin daurin wata biyar a gidan gyaran hali a matsayin hukuncin laifin da ya aikata, ko kuma zabin biyan tarar N200,000.
An tasa keyar G-Fresh zuwa gidan kaso ne sakamakon cin mutuncin Naira a cikin wani bidiyo da aka ɗauka a shagon wata yar TikTok mai suna Rahama Sa’idu da ke unguwar Tarauni.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


