Jarumar Fim Ta Fadi Yadda Ta Ganta a Aljanna bayan ta Mutu kafin Dawowa Duniya

Jarumar Fim Ta Fadi Yadda Ta Ganta a Aljanna bayan ta Mutu kafin Dawowa Duniya

  • Fitacciyar 'yar fim Doris Ogala ta ba da labarin yadda ta mutu, ta je aljanna, amma Ubangiji ya ce ta dawo duniya lokacinta bai zo ba
  • A cewarta, ta shiga aljanna inda ta ji dadin rayuwa, kuma ta zama sarauniya tare da bayi da zinariya a ko ina a cikinta
  • Doris Ogala ta bayyana cewa ta mutu kwanaki kadan da suka wuce, Ubangiji ya ba ta dama ta biyu don ta dawo duniya
  • Masoyanta a Instagram sun cika da godiya da fatan alheri a gareta, inda suka roki Ubangiji ya ci gaba da kare lafiyarta

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Ikeja, Lagos - Fitacciyar 'yar fim, Doris Ogala ta bayyana yadda ta mutu kwanaki ƙadan da suka wuce.

Jarumar ta ce bayan ta mutu, ta je aljanna kafin a ce mata ta dawo duniya domin lokacinta bai yi ba tukuna.

Kara karanta wannan

Sabuwar wakar caccakar Tinubu ta tayar da kura a Najeriya

Yadda jaruma ta mutu ta dawo duniya
Jarumar fim, Doris Ogala ya bayyana yadda ta tsinci kanta a aljanna bayan ta mutu. Hoto: @dorisogala.
Asali: Instagram

Yadda jaruma ta tsinci kanta a aljanna

Hakan na kunshe a wani sakon da jarumar ta wallafa a Instagram ranar Alhamis 10 ga watan Afrilun 2025 da muke ciki.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ogala ta ce an umurce ta da ta dawo duniya domin lokacin mutuwarta bai yi ba bayan ta shiga cikin aljanna a lahira.

Jarumar ta ce aljanna wuri ne mai nutsuwa, duk wata damuwa ta fita, kuma ta zama sarauniya tare da bayi da zinariya a kusa da ita.

Ta rubuta cewa:

“Watakila ba ni da lokaci mai yawa yanzu, dole na fada gaskiya, na mutu kwanaki kadan da suka gabata Ubangiji ya ba ni dama ta biyu.”
Jaruma ta fadi yadda ba ya umarni ta dawo duniya bayan ta mutu
Jarumar Nollywood, Doris Ogala ta ce har ta shiga aljanna aka dawo da ita duniya. Hoto: @dorisogala.
Asali: Instagram

Jarumar fim ta dawo duniya bayan mutuwa

Jarumar ta nuna wani dan bidiyo lokacin da abin ya faru a shafin inda ta fadi yadda aka ba ta umarni ta dawo duniya domin lokacinta bai yi ba tukuna, ta kara da cewa:

Kara karanta wannan

Abin al'ajabi: Wata yarinya da aka yi jana’izarta a Kano ta dawo gida da ranta

"Na mutu kamar yadda kuke gani na nan, na mutu da jikina, amma na kasance a aljanna.”
“Ubangiji ya ce min, ‘yata koma duniya, ba lokacinki ba ne yanzu', na ga kaina a aljanna cike da nutsuwa da kwanciyar hankali.”
"Ba na son dawowa, saboda dadin da nake ji ba misaltuwa ba ne, na zama sarauniya, na samu bayi da zinariya a ko’ na.”

Amma ta bayyana cewa, an ratsa ta ta wani kyakkyawan hanya sannan aka fada mata cewa:

“Ba lokacin ki bane yanzu, ki jira lokacinki kafin ki dawo."

Yadda yarinya ta dawo duniya bayan ta mutu

Mun ba ku labarin abin al'ajabi da ya faru a Kano yayin da aka ce wata yarinya da ta rasu kuma aka birne ta a watan azumin Ramadan din da ya wuce, ta dawo gida da ranta.

Wani matashi mai suna Kwamared Usama Lere ya ce ya je garin Kura domin tabbatar da gaskiyar batun, ya tarar da mutane suna tururuwar ganin yarinyar.

Lamarin ya ba da mamaki, ya jawo martanin jama'a sosai, wasu na ganin cewa ba ita ce aka binne ba, yayin da wasu ke ganin lamarin karya ne kawai.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.

Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng

iiq_pixel