Gawa ta mike: Ya mutu ya dawo
– Wani Dattijo ya mike daga cikin akwatin kabarin sa yayin da ake masa jana’iza
– Tsohon mai shekara 75 ya mutu ya dawo
– Wannan abu ya ba Jama’a mamaki
Wani Tsoho mai shekaru 75 a Duniya ya farka ya samu kan sa a cikin kabari ana shirin birne sa. Wannan abu dai ya faru ne da wani Dattijo mai suna Huang Mingquan a Kasar Sin watau Kasar China.
Kamar yadda Jaridun Kasar China suka rahoto, wannan tsoho yana mikewa sai ya fara tambayar ‘me ke faruwa a nan?’ ‘Wai birne ni za ku yi…?’ Wannan Tsoho dai ya samu kan sa a kudundune cikin akwatin katako na gawa tare da ‘Yan uwa da abokan arziki a zagaye da shi ana jana’iza.
KU KARANTA: Boko Haram: An saki mutane fiye da dubu
Wannan Mutumi dai yayi doguwar suma ne watakila, bayan da aka lura ya daina numfashi sannan kuma jikin sa yayi sanyi, sai aka dauka cewa ya rasu ne. Nan take ‘ya ‘yan sa da jikoki suka fara shirin birne sa.
Sai dai bayan kusan awanni takwas wannan mutumi ya farka, sai aka gan sa kawai dame-dame a kan akwatin gawan da ya ke ciki. Wannan abu dai da ya faru a Garin Junlian na Kasar China ya ba Jama’a mamaki.
Domin karin bayan a biyo mu a shafin mu na https://twitter.com/naijcomhausa da kuma https://www.facebook.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng