Rahama Sadau Ta Fadi Abubuwan da ke Burge Ta kan Sanusi II da Suka yi Wata Haduwa

Rahama Sadau Ta Fadi Abubuwan da ke Burge Ta kan Sanusi II da Suka yi Wata Haduwa

  • Tauraruwar Kannywood, Rahama Sadau, ta hadu da Muhammadu Sanusi II a filin jirgi, inda ta bayyana jin daɗinta
  • Martaninta ya jawo abin magana iri-iri a shafukan sada zumunta, inda mutane suka tofa albarkacin bakinsu
  • Wasu sun yaba da yadda ta nuna girmamawa, yayin da wasu suka ce tana da ƙauna ta musamman a gare shi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Kano - Jaruma a masana'antar Kannywood, Rahama Sadau ta bayyana jin daɗinta da girmamawa ga Muhammadu Sanusi II.

Jarumar ta bayyana cewa ta hadu da mai martaba Sanusi II ne a filin jirgin sama da suka hadu babu tsammani.

Rahama Sadau
Rahama Sadau ta hadu da Sanusi II. Hoto: Masarautar Kano|Rahama Sadau
Asali: Facebook

Legit ta tattaro bayanan da Rahama Sadau ta yi ne a cikin wani sako da ta wallafa a shafinta na Facebook ranar Alhamis.

Kara karanta wannan

An yi amfani da sunan matar gwamnan Katsina, an damfari mutane Naira miliyan 197

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Rahama Sadau ta hadu da Muhammadu Sanusi II

Fitacciyar jarumar Kannywood, Rahama Sadau, ta bayyana yadda ta gamu da Muhammadu Sanusi II a filin jirgin sama.

A cewarta, har abada za ta ci gaba da goyon bayansa saboda kamala, kwarjini da kuma halayensa na mutuntawa.

A cikin sakon da ta wallafa, Rahama ta bayyana cewa tana girmama Sanusi kuma za ta cigaba da goyon bayansa.

Jarumar ta ce:

"Na haɗu da Mai martaba Sanusi Lamido Sanusi a filin jirgi yau. Ma shaa Allah, haduwa da shi ko yaushe abin farin ciki ne a gare ni.
"Kwarewarsa, kwarjinin sa, dattakunsa marasa misaltuwa ne. Har abada zan kasance mai goyon bayansa!!!!"

Martanin mutane kan kalaman Rahama Sadau

Bayan wallafa sakon nata, masu amfani da shafukan sada zumunta sun tofa albarkacin bakinsu dangane da haduwarta da Muhammadu Sanusi II.

Wata mai amfani da Facebook, Bintu Bawa ta ce:

Kara karanta wannan

Matawalle: Ministan tsaro ya canja salon raba tallafin azumi, ya ba da N500m

“Kai! Wannan abin farin ciki ne! Ina jin yadda kike jin daɗin haduwa da shi daga kalamanki. Kin samu damar yin magana da shi ko dai kallon sa kawai kika yi?”

Sharifat Musa Abubakar kuwa ta ce:

“Da dai ki fito fili ki faɗi cewa kin kamu da soyayyarsa. Kada ki yi ta zagaye-zagaye.”

Wasu sun yaba da girmamawar da ta nuna

Dan Sarki Daura ya nuna farin cikinsa kan yadda Rahama ta bayyana girmamawarta ga Muhammadu Sanusi II. Ya ce,:

“Abin farin ciki ne haduwa da shi. Ina da tabbacin cewa ya ji daɗin yadda kika nuna masa girmamawa.”

Saif Sani Abdallah kuwa ya yaba da girmamawar da Rahama ta nuna, inda ya ce:

“Mun gode da yadda kika mutunta Sarkinmu! Allah ya mutunta ki ke ma.”

Anaemeje Igoche Catherine ta bayyana cewa ita ma tana girmama Muhammadu Sanusi II:

“Tabbas, ina girmama shi ni ma. Ina fatan kin yi tafiya lafiya.”

Kara karanta wannan

'Farashin abinci da fetur ya sauka a Najeriya': Minista ya zayyano alheran Tinubu

Abubakar Yusuf Ibrahim ya ce:

“Ai Sarki na kowa ne. Ran Sarki ya dade.”

Kareemah Bashir A. Abba kuwa ta roki Rahama Sadau da cewa:

“Idan kin sake haduwa da shi, don Allah ki mika masa gaisuwata.”

Rahama Sadau ta gana da ministoci

A wani rahoton, kun ji cewa jarumar Kannywood Rahama Sadau ta ziyarci ministocin tsaro da na yada labarai a birnin tarayya Abuja.

Rahotanni sun nuna cewa jarumar ta gana da su ne domin neman goyon baya kan wasu shirye shirye da take yi da suka shafi al'adun Arewa.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng

Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng