Soyayya Ruwan Zuma: Ƴar Majalisa Za Ta Auri Fitaccen Mawakin Najeriya, An Ga Bidiyo

Soyayya Ruwan Zuma: Ƴar Majalisa Za Ta Auri Fitaccen Mawakin Najeriya, An Ga Bidiyo

  • Fitaccen mawaki, Innocent Idibia ya miƙa zoben neman auren 'yar majalisar Edo, Natasha Osawaru, bayan sun yi rawa tare a bidiyo
  • Natasha ta amince da auren mawaki 2Baba bayan ta karbi zoben neman auren, wanda ya jawo ce-ce-ku-ce a kafofin sada zumunta
  • Mawaki 2Baba ya nemi auren 'yar majalisar ne kwanaki kusan 17 bayan ya sanar da rabuwarsa da tsohuwar matarsa Annie Idibia

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Edo - Fitaccen mawaki, Innocent Idibia (2Baba), ya durkusa har kasa, ya nemi auren 'yar majalisar jihar Edo, Natasha Osawaru.

A cikin wani faifan bidiyo bidiyo da ya karaɗe kafafen sada zumunta ranar Alhamis, 2Baba da Natasha sun nunawa duniya soyayyar da ke tsakaninsu.

2Baba ya mika zoben soyayyar neman auren 'yar majalisar Edo
Mawaki, 2Baba da 'yar majalisar Edo sun amince za su auri junansu. Hoto: @GistLovers
Asali: Twitter

2Baba ya nemi auren 'yar majalisa

A bidiyon, wanda jaridar Punch ta wallafa, an ga masoyan suna rawa cikin annashuwa tare da abokansu, inda daga bisani 2Baba ya miƙa mata zoben neman aure.

Kara karanta wannan

"Tinubu zai sha wahala": LP ta bayyana wanda za ta tsayar takarar shugaban ƙasa a 2027

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Bayan karɓar zoben, su biyun sun rungumi juna na tsawon lokaci, abin da ya jawo ce-ce-ku-ce a kafafen sada zumunta.

Wannan lamari ya biyo bayan rabuwar aure tsakanin 2Baba da tsohuwar matarsa, Annie Idibia, inda ya bayyana shirin sabuwar rayuwa da Natasha.

2Baba ya wanke Natasha daga zargi

Tun da farko, alamu na soyayya tsakanin su sun fara bayyana bayan 2Baba ya ziyarci majalisar jihar Edo da kuma wani bidiyonsu a wani gidan rawa a Legas.

A kokarinsa na fayyace gaskiya, mawaki 2Baba ya wallafa bidiyo a shafinsa na Instagram ranar Talata domin yin karin bayani kan lamarin.

Ya bayyana cewa an yi masa kazafi da sharri, ana zargin Natasha da kasancewa silar rushewar aurensa da Annie.

Mawaki 2Baba ya jaddada soyayyarsa ga Natasha

2Baba ya shaidawa duniya cewa:

“Hon. Natasha tana da kima da basira, ba ta da hannu a matsalolin da suka jawo mutuwar aurena da Annie ."

Kara karanta wannan

'Zan aure ta': Fitaccen mawakin Najeriya ya kamu da soyayyar 'yar majalisa

Ya kara da cewa,

"Na so Natasha sosai, tana da kyau, tana da kirki, kuma ina son aureta."

Wannan ikirarin ya jawo martani daban-daban daga mabiyan kafafen sada zumunta, wasu na yaba masa, yayin da wasu ke sukar wannan sabon mataki.

A yanzu, mutane na jiran matakin da za su dauka a wannan sabon salon rayuwar mawakin da ‘yar majalisar jihar Edo.

Kalli bidiyon a kasa:

Mawaki 2Baba ya tuba da dirkawa mata ciki

A wani labarin, mun ruwaito cewa, fitaccen mawaki, Innocent Idibia wanda aka fi sani da 2Baba, ya ce ya tuba daga dabi'ar yi wa 'yan mata ciki.

Mawaki 2Baba, ya bayyana hakan ne cikin wata bidiyo da ta bazu a dandalin sada zumunta yayin bikin Idoma International Carnival.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.

iiq_pixel