Bidiyo: Yadda Jarumin Nollywood Ya Koma Sana'ar Gyaran Famfo a Ƙasar Kanada

Bidiyo: Yadda Jarumin Nollywood Ya Koma Sana'ar Gyaran Famfo a Ƙasar Kanada

  • Fitaccen jarumi kuma mai shirya fina-finan Najeriya, Chris Bassey, ya bayyana cewa ya sauya sana'a bayan ya koma kasar Canada
  • Jarumi Bassey ya ce ya hakura da daukakar da ya ke da ita a harkar fim, ya kama sana'ar gyaran famfo tun bayan komawarsa Kanada
  • A zantawarmu da Abdul M. Shareef, wani jarumi a masana'antar Kannywood, ya koka cewa matsin tattali ya shafi harkar fim a yanzu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Kanada - Rahotanni sun bayyana cewa jarumi kuma mai shirya fina-finai a Nollywood, Chris Bassey, ya kama sana'ar gyaran famfo bayan ya bar Najeriya zuwa Canada.

Wannan dai na zuwa ne yayin da 'yan Najeriya da dama ke tafiya ci rani Kanada da sauran wasu kasashen ketare sakamakon matsin tattalin da Najeriya ke fuskanta.

Kara karanta wannan

"Na rasa uwa": Jonathan ya fadi alherin da marigayiya Hajiya Dada ta yi masa

Jarumin Nollywood, Chris Bassey ya yi magana kan sana'ar da ya koma yi a Kanada
Chris Bassey, jarumin fina finan Najeriya ya koma mai gyaran famfo a Kanada. Hoto: iamchrisbassey
Asali: Instagram

Jarumi ya koma gyaran famfo

Da yake magana yayin tattaunawar kai tsaye da Daddy Freeze a Instagram, ya jaddada cewa ya fi samun kudi a sabon aikinsa fiye da ayyukan da ya yi a baya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Lokacin da Daddy Freeze ya tambaye shi wace sana’a ce ya koma yi a Kanada, Bassey ya amsa da cewa:

“Na koma sana'ar gini a nan. Harkar gine gine na koma yi. Yanzu ni mai gyaran famfo ne."

"Dalilin komawa gyaran famfo" - Bassey

Daddy Freeze wanda ya yi mamakin jin hakan, ya tambayi fitaccen jarumin dalilin kama sana'ar aikin famfo da ya koma duk da shahararsa.

Bassey ya ba shi amsa cikin harshen pidgin:

"A cikin watanni bakwai da suka gabata, lardin da na ke ziyarta a karshen makonni a Kanada, ko mai sana'ar da ta shafi fasaha ba zai iya kashe wannan kudin ba.

Kara karanta wannan

'Abin da ya sa Dangote ba zai siyar da mai kasa da farashin kamfanin NNPCL ba'

"Wannan fa ina maka magana ne a kan Kanada, ba ni da masaniyar kudin da masu gyaran famfo ke samu a Amurka ko Birtaniya."

"Matsin tattali ya shafi fim" - Abdul

A zantawarmu da fitaccen jarumin Kannywood, Abdul M Shareef, ya bayyana cewa matsin tattalin arzikin da ake fama da shi ya yi tasiri a harkar nishadi a Najeriya.

Abdul M. Shareef ya ce akwai masu shirya fina finai da dama da a yanzu ba su da jarin shirya fim ko daya, sakamakon karyewar tattalin da kuma tsadar rayuwa.

Jarumin ya bukaci gwamnatin tarayya da ta zuba jari a masana'antar fina finan Kannywood wanda a cewarsa hakan zai jawo mata kudaden shiga idan kasuwar ta daidaita.

Game da ficewar jarumai da mawaka zuwa kasashen ketare ci rani, Abdul M Shareef ya ce ma damar lamura za su ci gaba da tafiya a haka, to mutane da dama za su nemai damar ficewa.

Kara karanta wannan

'Abin da ya sa bai kamata Goodluck Jonathan ya sake neman takara a 2027 ba'

Kanayo ya gabatar da dansa a fim

A wani labarin, mun ruwaito cewa fitaccen jarumin fina finan Kudancin Najeriya, Kanayo O. Kanayo ya gabatar da dansa Clinton Mbaise a masana'antar Nollywood.

Kanayo na so dansa ya gaje shi a harkar fim inda ya gargadi masu shirya fina finan da su yi mu'amala da yaron nasa ba tare da wani fifiko ba yayin da zai rika aiki matsayin mataimakinsa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.