Neman halal: A baya gyaran ruwa na ke yi inji Gwamnan Legas, Sanwo-Olu

Neman halal: A baya gyaran ruwa na ke yi inji Gwamnan Legas, Sanwo-Olu

- Gwamnan Jihar Legas ya ce ya taba yin aikin gyaran ruwa a shekarun baya

- Jide Sanwo-Olu ya ce ya yi wannan aiki ne kusan shekaru 30 da su ka wuce

- Gwamnan ya bayyana haka wajen yaye daliban da aka koyawa aikin hannu

Mai girma gwamnan jihar Legas, Babajide Sanwo-Olu, ya bayyana cewa ya yi aikin hannu domin ya samu na kai wa baka.

Babajide Sanwo-Olu ya ke cewa a shekarun baya ya kasance ya na aikin famfo, watau ya taba zama malamin gyaran ruwa.

Mista Babajide Sanwo-Olu ya yi wannan bayani ne a lokacin da ya yaye mutane 6, 252 da aka koyawa sana’ar hannu.

KU KARANTA: Tarihin Babajide Sanwo-Olu

Gwamnatin jihar Legas ta dauki nauyin koyawa dalibai fiye da 6, 000 aikin hannu a cibiyoyin koyon sana’a 18 da ke fadin jihar.

Gwamnan ya yi kira ga matasa da matan da aka koyawa wadannan aiki da su yi amfani da wannan dama da su ka samu da kyau.

Sanwo-Olu ya fadawa wadannan dubunnan mutane da aka yaye, su kafa kansu, har su dauki wasu aiki, maimakon jiran gwamnati.

Mai girma gwamnan ya ce ya yi wannan aiki na washe ne shekaru kimanin 30 da su ka wuce.

Neman halal: A baya gyaran ruwa na ke yi inji Gwamnan Legas, Sanwo-Olu
Sanwo-Olu ya yi aikin washe a 1990s
Source: Facebook

KU KARANTA: APC za ta lashe zaben Ondo - Gwamnan Legas

Mista Sanwo-Olu ya fadawa daliban da aka yaye cewa su rika kokarin kara samun gogewa a kan aikinsu domin su bunkasa sana’ar.

An horas da daliban ne kan harkar gyaran gashi, aski, kwalliya da gyaran jiki, girke-girke, aikin otel, dinkin kaya da hula, da aikin takalma.

Ko da ya yi gyaran ruwa, gwamnan yana da digiri da digirgir daga jami’ar Legas, sannan ya yi karatu a Landan kafin shiga siyasa a 2003.

Rahotanni sun zo kwanaki cewa Mai girma Babajijde Sanwo-Olu ya bada umurnin bude duk wasu masallatai da dakunan ibada da ke Legas.

An bude masallatai domin a rika yin sallolin yini, haka kuma sauran wuraren ibada na mako.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit.ng

Online view pixel