“Na Yi Lalata da Maza Sama da 3000”: Jarumar Fim Ta Yi Maganar Karfin Sha’awarta

“Na Yi Lalata da Maza Sama da 3000”: Jarumar Fim Ta Yi Maganar Karfin Sha’awarta

  • Da karfin gwiwarta, fitacciyar jarumar fina-finan Nollywood, Esther Nwachukwu ta bayyana wasu bayanai masu rikitarwa game da rayuwarta
  • A wata zantawa da aka yi da tauraruwar fina-finan a shirin 'Honest Bunch', ta bayyana irin karfin sha'awarta
  • Ta kuma ba da taƙaitaccen bayani game da garuruwa da ƙasashen da ta je ta yi lalata da mazajen da suka kai kimanin 3000 a cikin shekaru 30

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Fitacciyar jarumar fim ta Najeriya, Esther Nwachukwu, wacce aka fi sani da Esther Sky, ta jawo ce-ce-ku-ce a yanar gizo bayan da ta fadi rayuwar jima'inta.

Esther Nwachukwu ya bayyana cewa ita tana lalata ne da mazaje masu aure ba wai samari ba, kuma ta kwanta da mazan da ba ta san iyakar adadinsu ba.

Kara karanta wannan

"Da hankalina," Matar da ta kekketa fasfon mijinta a filin jirgi ta fadi dalilin hakan

Jarumar fim, Esther Nwachukwu ta yi magana kan kwana da mazaje 3,000
Jarumar fim, Esther Nwachukwu ta yi magana akan mazan da ta yi lalata da su. Hoto: @esthersky77
Asali: Instagram

Jarumar fim ta yi lalata da mazaje 3000

A wata hira da aka yi da ita a kwanan nan a shirin Nedu Wazobi na 'Honest Bunc', Estagr Nwachukwu ta yarda cewa ta kwanta da mazaje sama da 3,000.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ta kara da cewa ta yi lalata da mazajen auren ne a yawon duniya da ta yi kama daga Najeriya zuwa Cyprus, Turkiyya, Kenya, har zuwa Ghana.

Jarumar fim din ta ce:

“Ba zan iya tuna adadin mazajen da na kwanta da su ba. Suna da matukar yawa gaskiya."

Mai gabatar da shirin ya tambaye ta:

"Sun kai 3,000?"

Esther ta ba shi amsa da cewa:

“Ya fi haka. Na yi lalata da mazaje daga Najeriya, Cyprus, Turkiyya, Kenya, Ghana, da sauransu. Ba na kwanciya da samari, kawai ina da lalata da mazajen aure ne."

Kara karanta wannan

Uju Kennedy: Mamaki ya kama jama'a bayan Ministar harkokin mata ta tarwatsa taro

Kalli yadda ta yi magana a kasa:

Esther Nwachukwu ta jawo ce-ce-ku-ce

Legit Hausa ta tattaro martanin a kasa:

iameniolamyde:

"Shin Nedu jakadan kowane gidan masu tabin hankali ne? Yadda yake zakulo masu tabin hankali yana hira da su yake bani mamako koyaushe."

b_uniqu.e':

"Yanzu na gaskata cewa da gangan Nedu ya ke yin hira da irin wadannan mutanen, kawai yana yi ne domin ya jawo masu kallo."

ada_amakassy:

"Wannan tana bukatar a yi mata magani, ba wai a yi hira da ita ba."

_iamsheila__:

"Yar uwa al'aurarki yanzu ta koma kamar kasuwa. Kawai ki kai shi wajen gwamnati su sanya shi a gidan yawon bude ido ana biya ana kallo."

Budurwa ta rasa aiki saboda lalata da maza

A wani labarin, mun ruwaito cewa shahararriya a shafin OnlyFans, Annie Knight ta rasa aikinta bayan da aka gano tana kwana da tulin maza.

Kara karanta wannan

Yunwa na barazana ga rayukan almajiran Kano, an roki matasa su hakura da zanga zanga

A kwanakin baya aka ruwaito Knight ta yi hira a shirin The Kyle and Jackie O inda ta yi bayanin yadda ta ke kwana da mazaje 300 a shekara, wadanda da yawansu ba ta san asalinsu ba.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.