Wata budurwa ta bakunci lahira yayin da take lalata da saurayinta a mota

Wata budurwa ta bakunci lahira yayin da take lalata da saurayinta a mota

  • Rahoto daga kasar Brazil ya bayyana cewa, wata budurwa ta mutu yayin da take lalata da saurayinta
  • Rahoton ya bayyana cewa, budurwar ta mutu ne sanadiyyar bugawar zuciya lokacin da suke tare
  • An garzaya da ita asibiti, wanda tuni likitoci suka fara bincike, inda suka gano babu alamar cin zarafinta

Brazil - Mutuwa ta dauke wata budurwa mai suna Gabrielly Dickson a yayin da suke tsaka da fasikanci da saurayinta mai shekaru 26 a cikin mota.

An garzaya da budurwar mai shekara 15 zuwa asibiti ne bayan saurayin nata da yake fasikanci da ita ya lura cewa ta fita daga hayyacinta, in ji Aminiya.

’Yan sanda da ke binciken lamarin sun ce saurayin, wanda ake kira “babban mai taimako”, ya shaida musu cewa yana cikin saduwa da ita a cikin mota ne ya lura labbanta da fatar jikinta sun koma fari fat, hannuwanta kuma sun jujjuye.

Kara karanta wannan

Buhari ya tausawa wadanda ambaliyar ruwa ta yi wa barna, ya ce zai taimaka musu

Wata budurwa ta bakunci lahira yayin da take lalata da saurayinta a mota
Hoton budurwar da ta sheka | Hoto: dailymail.co.uk
Asali: UGC

Ko da aka kai ta asibiti, likitoci sun gano zuciyarta ta buga, amma babu yadda suka iya, washegari da safe kuma ta sheka lahira.

Yaya dangi da abokan arziki suka ji da samun labarin mutuwar?

Labarin mutuwar buduwar a yayin da suke fasikanci da saurayinta ya girgiza ’yan uwa da abokan arziki da ma makwabta a unuguwar Cubatão da ke birnin São Paulo na kasar Brazil.

A halin yanzu, likitoci a asibitin suna gudanar da bincike a kan gawar domin gano tabbatar da ainihin musabbabin mutuwarta, ’yan sanda kuma na nan suna jiran sakamako.

Iyayenta sun shaida wa ’yan sanda cewa ’yarsu ba ta fama da matsalar bugun zuciya kuma ba su san saurayin nata ba.

Likitocin a asibitin na UPA Jardim Casquiero da ke yankin na Cubatão sun ce a gwajin farko da suka yi an samu jini a cikin al’aurar budurwar, amma babu alamar an ci zarafinta.

Kara karanta wannan

Hotuna da bidiyon mutumin da ya auri mata biyu a rana daya, an yi masu ruwan N20

A kasar Brazil, an amince mace mai shekaru 14 ta iya kusantar namiji, wanda wannan yasa ba kama saurayin nata da laifin komai ba, kamar yadda Daily Mail ta ruwaito.

Gaskiya: Yadda matashi ya mayar da 2500000 da aka tura asusun bankinsa cikin kuskure

A wani labarin daban, wani matashi dan Najeriya mai kwatanta gaskiya, Julius Eze, ya sha yabo a kafafen sada zumunta makonni da suka gabata saboda mayar da N2.5m da aka aika zuwa asusunsa, ya kuma fito ya yi magana game da lamarin.

A wata hira ta musamman da Legit.ng ta yi dashi, Julius ya bayyana cewa duk da yana da bukatu a lokacin da aka kuskure tura kudin asusunsa, bai ji a ransa yana son rike kudin ba.

Ban yi tunanin rike kudin ba

Ya ce:

“Ban yi niyyar rike kudin ba ko amfani da su don amfanin kaina. Na san ba nawa ba ne kuma babu wanda nasan zai aiko min da irin wannan a lokacin da suka shigo.”

Kara karanta wannan

Kisan matafiya a Filato: Yadda Kiristoci, 'yan adaidaita da sojoji suka cece mu, Matafiyi

Julius ya ce danginsa sun yaba masa kan abin da ya yi, inda ya kara da cewa mahaifinsa ma ya kira don bayyana yadda yake alfahari da kasancewar dansa mai gaskiya kamar sa.

Lokacin da aka tambaye shi kan yadda aka bashi kyauta bisa aikin da ya yi, matashin ya ce mai kudin ya ba shi N50,000, lamarin da ya faranta masa rai matuka.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.