Abin yayi yawa: An kama 'yar fim da take kwanciya da miji sannan kuma tayi madigo da matarshi
- Wata ma’abociya amfani da kafar sada zumuntar zamani ta yi wa wata ‘yar wasn kwaikwayo terere
- Ta bayyana cewa, Angela Okorie ta sha dukan da aka yi mata ne bayan da aka kamata da kwartanci
- Ta ja kunne ‘yam mata da su kiyayi kosawa da kuma bibiyar mazan mutane don samun abun duniya
Wata budurwa ‘yar Najeriya mai amfani da suna @ifeoluwa.oluwa.712 a shafinta na Intsagram ta zargi cewa, an hari ‘yar wasan kwaikwayo Angela Okorie ne saboda an kamata tana lalata da mata da miji.
Ify Okoye ta wallafa a shafinta yadda da yawan ‘yan wasan kwaikwayon mata suke karuwanci. A yayin mayar da martani, Ify ta ce dalilin da yasa aka hari Angela bai wuce neman batawa mutumin suna da take yi ba bayan kuma tana lalata dashi da matarshi.
Ify Okoye ta wallafa: “Idan har na kira wata ‘yar wasan kwaikwayon Najeriya da karuwa, kuma wani ya zo harata, idan na zabga mishi mari, sai ya ga taurari. Angela da kanta ta jawo wannan harin da aka yi mata. Ta ki barin gidan matar, bata kuwa da wani abu da ya wuce ta jijjiga karin gashin da ke kan Angela. Daga girgizata ne fa har hankalinta ya tashi. ‘Yam mata a rabu da mazan aure!!!”
KU KARANTA: Cin barkono yana kare mutane daga mutuwa ta hanyar bugun zuciya - Bincike
A yayin mayar da martani gareta, wata ma’abociyar amfani da kafar sada zumuntar zamanin ta wallafa: “Kosawa! Kowa tana son tuka mota mai tsada kuma da rayuwa a Lekki. Tana lalata da mata da mijinta duk su biyun. Mijin na zama a Najeriya inda matar ke zama a Amurka. Matar ta gano hakan kuma ta harzuka. Daga nan sai aka fara fada. Daga nan sai angela ta fara neman bata musu suna.
“A neman rufin asiri, mijin ya biyata $20,000, itama matar ta biya $10,000 bayan da suka ja kunnen Angela da kada su kara ganinta kusa da gidansu. Angela bata ji jan kunne ba. Idonta ya rufe sai ta samu kudi. Kada ku tambayeni yaya aka yi na sani, don inada mai kawo min labari daga cikin gidan masu kudin.”
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng