Bayan Dawowa Sarauta, Ɗan Sanusi II Zai Auri Ƴar Babban Ɗan Siyasa a Najeriya
- Duk da ana tsaka da rikicin sarautar Kano tsakanin Muhammadu Sanusi II da Aminu Ado Bayero, an saka auren Ashraf Lamido
- Rahotanni sun nuna cewa a watan Agusta mai kamawa ne za a daura auren Ashraf da ƴar wani babban dan siyasar Najeriya
- Wannan shi ne biki na farko da za a yi Gidan Dabo tun bayan dawowar mai martaba Muhammadu Sanusi II karagar mulki
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Kano - Shirye shiryen bikin Ashraf Adam Lamido sun fara kammala yayin da aka sanya ranar aurensa a watan Agusta.
Rahotanni sun bayyana cewa za a daura auren Ashraf Lamido ne da amaryarsa mai suna Sultana Nazif.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa Ashraf Lamido zai auri ƴar babban ɗan siyasa ne daga jihar Bauchi a Najeriya.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Yaushe za ayi auren Ashraf Sanusi II?
Rahotanni sun yi nuni da cewa a ranar 2 ga watan Agustan wannar shekarar ne za a daura auren Ashraf Lamido da Sultana Nazif.
Hakan biyo bayan sake zafafan hotunan shirin daurin auren da amarya da ango suka yi ne a kafafen sada zumunta.
A ina za a daura auren ɗan Sanusi II?
Rahotanni sun nuna cewa za a daura auren ne a babban masallacin kasa da ke birnin tarayya Abuja.
Wannan kuma shi ne karon farko da za daura aure a Gidan Dabo tun dawowar Muhammadu Sanusi II kan karaga.
Waye mahaifin Sultana Nazif?
Mahaifin Sultana Nazif ya kasance shahararren dan siyasa ne da ya fito daga jihar Bauchi a Arewa maso gabas.
Senata Dakta Sulaiman Mohammed Nazif ya kasance dan kasuwa ne kuma ya wakilci Bauchi ta Arewa a majalisar Dattawa a shekarar 2007.
Sanusi II ya yi umurnin dasa bishiya
A wani rahoton, kun ji cewa sarkin Kano, Muhammad Sanusi II ya kasance babban bako yayin kaddamar da shuka bishiyoyin da gwamnan Kano ya yi.
Mai martaba Muhammad Sanusi II ya ba masu rike da sarautu umurni kan yadda ya kamata su bayar da gudunmawa wajen nasarar shirin.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng