An kira Musulmai suyi riko da Al-Kur’ani
Wasu Malamai daga kasar Saudiyya sun yi kira ga Musulmai suyi riko da littafin Al-Kur’ani mai girma domin su rabota a nan Duniya da lahira.
Wasu Malaman addini da suka taso tun daga kasar Saudiyya sun yi kira ga Jama’a suyi riko da Littafin Al-Kur’ani mai girma. Malaman suka ce riko da littafin Allah ne kadai zai kai Jama’a ga shiriya Duniya da kuma Lahira.
Malaman dai sun taso ne daga Jami’ar Ummul-Qura ta cikin Birnin Makkah da ke Kasar Saudiyya inda suka zo Najeriya kuma Jihar Kaduna. Sun zabi wurare inda suka yi wa’azi a Jihar daga ciki akwai masallacin ITN da ke Zangon-Shanu Zaria.
KU KARANTA: Ga wani masallaci da fuskar coci
Dr. Ahmad Al-Furaih da kuma Dr. Ahmad Al-Huraisi da ke Jami’ar Birnin Makkah suka ce dole a komawa Littafin mai tsarki domin a samu cigaba a nan da ma gaba. Daya daga cikin Malaman yace idan har makarantun Kur’ani suka lalace to al’umma ta lalace koda yake dai mutanen Najeriya suna da kokarin karatun Al-kur’ani.
Dr. Al-Huraisi yayi kira da Jama’a su yi koyi da darussan da ke cikin Al-Kur’ani irin na kisosshin Annabawa. Riko da littafin dai bai tsaya a karatu ba kurum, ya hada har da aiki da shi Inji Malaman kamar yadda mutanen da su gabace mu suka yi.
Ku same a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Allah mai iko.
Asali: Legit.ng