An Daure ‘Yar Fim a Kurkuku Saboda Liƙi da Manna Sababbin Kudi a Wajen Biki

An Daure ‘Yar Fim a Kurkuku Saboda Liƙi da Manna Sababbin Kudi a Wajen Biki

  • Chukwujekwu Aneke ya yi hukunci a shari’ar hukumar EFCC da Oluwadarasimi Omoseyin a kotunsa
  • Tun a shekarar bara aka yi karar ‘yar fim din saboda ta wulakanta sababbin kudi a wajen wani biki
  • Laifin da Omoseyin ta aikata ya saba dokar da ta kafa bankin CBN, ya cancanci dauri ko biyan tara

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Lagos - Mai shari’a Chukwujekwu Aneke ya daure Oluwadarasimi Omoseyin saboda cin mutuncin sababbin kudi.

The Guardian ta ce an samu Oluwadarasimi Omoseyin wanda ‘yar wasan kwaikwayo ce da liki da taka Nairori.

Simi Gold
An samu Simi Gold da laifin likin kudi Hoto: @officialefcc, @darasimi0402
Asali: Instagram

Simi Gold tayi likin kudi a bikin Lekki

Hakan ta faru ne a wajen wani biki da aka shirya a yankin Lekki. A dalilin haka EFCC ta shigar da kara gaban kotu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kara karanta wannan

Rikita-rikita yayin da tsohon Akanta-janar ya tona asirin EFCC kan yarjejeniyarsu, ya fadi dalilai

Tun ranar 13 ga watan Fubrairun 2023 aka shiga kotun tarayya mai zama a garin Ikoyi da ‘yar wasar kwaikwayon.

Hukumar EFCC ta shiyyar Legas ta jefi tauraruwar da aikata laifuffuka biyu, zargin da ta musanya duka da farkon shari'ar.

Tun wancan lokaci aka bada belin Oluwadarasimi Omoseyin saboda ta yi ikirarin ba ta aikata laifin da ake zargi ba.

Shari'ar Simi Gold da EFCC

Lauyan da ya shigar da kara, Z.B. Atiku ya kira wani jami’in EFCC, Abubakar Mohammed Marafa ya kawo hujjoji.

Rahoton ya ce da Simi Gold ta ga irin hujjojin da aka nunawa kotu, sai ta amsa cewa ta aikata laifin da ake tuhuma.

Mohammed Marafa ya ce jami’an hukumar ICPC suka fara cafke Omoseyin a 2023, sai suka mika ta zuwa ga ‘yan EFCC.

‘Yar wasan ka shaidawa EFCC mai yaki da rashin gaskiya yadda ta halarci bikin wata kawarta da aka shirya a Lekki.

Kara karanta wannan

Mai ba Jonathan shawara ya nunawa Tinubu hanyar farfado darajar Naira kan Dala

Wanda ake kara ta yarda ta yi manni da sababbin kudi ‘yan N200 da N100, wanda laifi ne a sashe na 21 na dokar CBN.

'Yar wasar za ta je kurkuku?

Mai shari’a Aneke ya duba faifen bikin ya yankewa wanda ake kara hukuncin daurin watanni shida a gidan gyaran hali.

Sahara Reporters ta ce wanda ake kara za ta iya biyan tarar N300, 000 a madadin dauri.

Lauya mai bada kariya, Afuye Adegbola ya nemi sauki domin ba a taba samunta da laifi ba, kuma ta tuba, sannan tana da ‘ya.

Haduwar lauyan Tinubu da Obasanjo

Tsohon shugaban kungiyar lauyoyi na kasa, Wole Olanipekun ya bada labarin wata alakarsa da Olusegun Obasanjo a 2002.

Wole Olanipekun SAN ya bada shawarar a fito da sabon kundin tsarin mulki, a kan wannan ne Obasanjo ya kusa doke shi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng