Ba Su Fi Karfi Na Ba: Magidanci Mai 'Ya'ya 126 Ya Auri Mata Ta 11 Yana Da Shekaru 83

Ba Su Fi Karfi Na Ba: Magidanci Mai 'Ya'ya 126 Ya Auri Mata Ta 11 Yana Da Shekaru 83

  • Tsohon mai shekaru 83 ya auri mata karo na 11 duk da ya kasance mahaifin yara 126 da tarin jikoki
  • Magidancin ya ce kwakwalwarsa, kudinsa da suffarsa duk za su iya daukar dawainiyar da ke tattare da matan har da yaran
  • Da aka rarrabe 'ya'yan da ya haifa a duniya, a halin yanzu yana da yara maza 18, yara mata 20 da jikoki maza da mata 88

Saudiyya - Wani magidanci mai 'ya'ya 126 ya yi aure karo na 11 a rayuwarsa duk da kuwa yawan shekarun da yake da su a duniya.

Mutumin mai suna Ali Al Balawi 'dan kasar Saudi Arabia a halin yanzu yana da shekaru 83 a duniya.

Ali Balawi
Zan iya Kula dasu: Magidanci Mai 'Ya'ya 126 ya Auri Mata ta 11 Yana da Shekaru 83. Hoto daga Gulfnews
Asali: UGC

Ya yi shagalin bikinsa karo na 11 da wata gagagrumar liyafa kuma iyalansa da masoyansa tare da masu masa fatan alheri sun baibayeshi.

Kara karanta wannan

“Sadakina Ya Karu”: Matashiya Ta Dafa Kwai Karo Na Farko A Rayuwarta, Ya Fito Kamar Bayan Tukunya a Bidiyo

Da zuwa sabuwar amaryar, Ali yanzu yana da matan aure hudu a gidansa duk da cewa ya yi aure kari na 11 ne.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Bayani kan iyalansa da ke karuwa kullum ya nuna cewa, yana da yara maza 18, yara mata 20 da kuma jikoki mata da maza 88.

Zan iya kula da iyalina, Ali ya ce

Ya kare yawan iyalansa da cewa, yana da kudin da zai iya kula da su duk da cewa ya fara tsufa kuma shekaru sun tafi.

Ali ya ce duk da shekaru 83 da yake da su a duniya, yana da karfi na hankali, jiki da kudi da zai iya kula da tarin iyalansa da yake da su.

A maganar da ya yi da Gulfnews, ya ce:

"Babu abinda zai hana shi sake aure. Ina da kudi, lafiyar kwakwalwa da jiki da zan iya kula da mata hudu."

Kara karanta wannan

Dan Najeriya Ya Hana Fasinjoji Sauka Daga Jirgin Sama Bayan Ya Nemi Jakar Kilishinsa Ya Rasa, Bidiyon Ya Yadu

Yace bashi da matsalar aure saboda yana kula da matsan daidai da juna. Ali ya shawarci maza da su kara aure a irin wannan shekarun in har suna da lafiya.

Daily Trust ta rahoto cewar auren Ali karo na 11 an yi shi ne a Tabuka da ke arewa maso yammacin Saudi Arabia.

Matar aure ta haifa jinjiri rike da IUD

A wani labari na daban, wata mata mai suna Violet ta bayyana yadda bata shirya haihuwa ba bayan tayi aure amma taje tayi tsarin iyali.

Sai dai cike da abun mamaki, ta haifa yaro namiji bayan samun ciki kuma ya fito rike da IUD a hannunsa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel