Saurayina Yace Ina Kama da Gardi: Budurwa ta Nuna Canzawarta zuwa 'Yar Kwalisa

Saurayina Yace Ina Kama da Gardi: Budurwa ta Nuna Canzawarta zuwa 'Yar Kwalisa

  • Wata budurwa 'yan Najeriya ta je soshiyal midiya inda ta bayyana surarta ta yanzu tare da danganta ta da baya
  • Kamar yadda budurwar tace, saurayinta ya datse soyayyarsu inda yace tana kama da gardi a shekaru baya da suka wuce
  • Bayan shekaru, budurwar ta canza kwata-kwata inda ta koma gogaggar 'yar kwalisa, son kuwa kin wanda bai samu ba

Jama'a sun dinga martani kan wata kyakyawar budurwa wacce ta nuna siffarta ta baya a yanar gizo.

Budurwar ta bayyana a soshiyal midiya inda ta dinga tashe bayan ta bayyan dalilin da yasa saurayinta ya gujeta da kuma yadda ta koma yanzu.

Budurwa
Saurayina Yace Ina Kama da Gardi: Budurwa ta Nuna Canzawarta zuwa 'Yar Kwalisa. Hoto daga TikTok/(@_starrrr)
Asali: UGC

A yayin da ta je shafinta na TikTok, ta wallafa tsohon hotonta inda ta ke sanye da rigar kammala karatu inda tace saurayinta a wannan lokacin ya bar ta saboda yace tana kama da gardi.

Kara karanta wannan

Soyayya Gamon Jini: Dirarriyar Matar Aure ta Bayyana Wadan Mijinta a Bidiyo, Tace Suna Cikin Farin Ciki

Daga baya, ta bayyana wani kyakyawan hotonta wanda ta canza sam ba za a ce ita ce waccan ta baya mara salon ba, surarta kanta abun kallo ce.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Budurwar ta bayyana matsayin cikakkiyar 'yar kwalisa, son kowa kin wanda bai samu ba a sabon hotonta.

Kalla bidiyon:

Soshiyal midiya tayi martani

Samuel M Champion yace:

"Kin gani ko, a gaskiya gaskiyarsa ya fadi... Amma a cire wasa, kina da kyau."

_akanboi yace:

"Yanzu na gane dalilin da yasa nayi baki, kila idan nayi kudi gobe, duk wannan kalar za ta canza."

Daniel Dickson317 yace:

"Amma fa ba karya yayi ba."

Qwesi Dollar tace:

"A gaskiya ba karya yayi ba a baya, kawai da ya dan kara hakuri."

El_Martino360 yace:

"Ko dai wasa ki ke. Wanne irin wasa ne wannan kyakyawa."

Kara karanta wannan

Bidiyon Budurwar da ta Hau Jirgin Tun Daga Amurka har Nahiyar Afrika Don Siyan Man Kadanya Mai Kyau

Johnson Amankwah788 yace:

"Au a wannan matakin har ki na soyayya? Ke a lokacin da ke ce shi za ki tsaya?"

Tsoho ya bayyana shekarun da ya kwashe bai yi bacci ba

A wani labari na daban, wani tsoho a kasar Vietnam ya sanar da cewa rabonsa da ya runtsa bacci a rayuwarsa tun 1962, wanda hakan ke nuna shekaru 61 kenan.

Yana nan garau cikin koshin lafiya babu wani ciwo. Sai dai jama'a sun dinga tantama kan sahihancin labarin da yake bayyanawa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel