Bidiyon Dirarriyar Budurwa da Wadan Saurayinta ya Janyo Cece-Kuce

Bidiyon Dirarriyar Budurwa da Wadan Saurayinta ya Janyo Cece-Kuce

  • Wata dirarriyar budurwa ta watsu a bidiyon da tayi tana nuna mijinta wanda ya kasance wada mara tsawao
  • Budurwar tace ita da wadan mijinta suna cikin kwanciyar hankali da farin ciki yayin da suka karkasce suka dauka hotuna
  • Ma'abota amfani da dandalin TikTok sun bayyana goyon bayansu kuma jama'a na cewa sun mori rayuwar aurensu matukar akwai farin ciki

Wani gajeren bidiyo na wata dirarriyar mata da mijinta wanda ya kasance wada ne ya yadu kuma ya samu sama da masu kallo 300,000.

Mata da miji
Bidiyon Dirarriyar Budurwa da Wadan Saurayinta ya Janyo Cece-Kuce. Hoto daga TikTok/@www.kahboh.
Asali: UGC

Dirarriyar matar ta wallafa bidiyon a TikTok inda ta nuna yadda ita da mijinta ke jin dadin aurensu na soyayya.

Kyakyawar budurwa m.ai amfani da suna @www.kahboh ta hada hotunansu wanda ita da mijinta aka daukesu a wurare daban-daban.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kara karanta wannan

"Yanzu Yan Boko Haram Sun Koma Sanya Tufafin Mata Yayin Kai Hare-Hare" - Inji Ndume

A daya daga cikin hotunan, mijin yana tsaye a gabanta yayin da ita kuma ta saka hannayenta kan kafadarsa cike da nuna shaukin kauna da soyayya.

A wani hoto na daban kuwa, mutumin ya tsaya ta bayanta inda ya riko kugunta cike da soyayya da nuna kauna bayyane.

Jama'a a TikTok sun dinga bayyana yadda matar da mijinta suka birgesu. Tace dukkansu suna zaune cikin farin ciki.

Kalla bidiyon:

Martani daga ma'abota amfani da TikTok

@onyinyechi tace:

"Matukar kuna cikin farin ciki."

@daniloveya tambaya:

"Me ke hana ni aure ne?"

Gabriella Tiwaah tayi martani da:

"Ina fatan kada Ubangiji yasa wannan murmushin da ke fuskarku ya disashe."

@kingfish yace:

"Ko a makaranta ina yawan yin amfani da rage doguwar hanya."

@Winnie yayi tsokaci da:

"Matukar dai kuna cikin farin ciki kawata."

@Anita Ivie tace:

"Aw wannan soyayya ce ko. Huhuhuhuhu."

@Mommaslv2 tace:

Kara karanta wannan

Karin bayani: 'Yan daba sun sa wuta a hedkwatar hukumar INEC a wata jihar Arewa

"Wannan irin hayaniya da ke sashin tsokaci."

Alkali yasa budurwa ta biya tsohon saurayin diyyar N1m saboda kin aurensa

A wani labari na daban, wani alkali ya umarci wata bduurwa da ta biya tsohon saurayinta diyyar N1m saboda alkawarin aure da tayi masa amma ta fasa.

Budurwar ta ci kudin saurayin inda har kudin makaranta ya dinga biya mata amma ta ki aurensa baki daya, hakan yasa ya maka ta a gaban kotu.

Tuni jama'a suka dinga tsokaci kan wannan hukuncin da alkalin ya yanke inda wasu suka ce yayi daidai.

Asali: Legit.ng

Online view pixel