Bidiyo: Budurwa ta Dawo Afrika Tun Daga Amurka don Siyan Man Kadanya

Bidiyo: Budurwa ta Dawo Afrika Tun Daga Amurka don Siyan Man Kadanya

  • Wata mata ta taso takanas daga Amurka kawai don ta siya man kadanya da ta ke amfani da shi a can don kasuwanci
  • Ta wallafa bidiyon lokacin da ta shillaro da kuma lokacin da aka hada ma ta shi a wani salo na daban da zai birge jama'a
  • Tuni, masu amfani da kafar TikTok sun fara yabawa da irin kyan ganin da man kadan ke da shi a bidiyon da ke tashe

Masu amfani da kafar TikTok sun kasa rufe bakunansu bayan ganin yadda wata mata ta taso takanas daga Amurka kawai don siyan man kade gami da sake biyan kudin jirgin komawa.

Mai siyan man Kadanya
Bidiyo: Budurwa ta Dawo Najeriya Tun Daga Amurka don Siyan Man Kadanya. Hoto daga TikTok/@uncoveredbeauty_.
Asali: UGC

Sai dai, a bidiyon da ya yadu wanda ta wallafa, matar ta bayyana yadda ta shillo musamman din ta siya man kada saboda tana bukatar ingantacce.

Kara karanta wannan

Bidiyo:Matar aure ta Kama Mijinta Dumu-dumu da Budurwarsa a Wurin Cin Abinci, An Tafka Dirama

Ya fayyace yadda take bukata ingantaccen man kadanya don kasuwancinta daga Amurka.

A bidiyon, ta nuna lokacin da ta ke cikin jirgi da lokacin da aka tattara ma ta man kadanya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kamar yadda a bidiyon ta bayyana irin yadda man kadanyan ke da danko, wanda a ganinta shi ne ingantacce daga nahiyar iyaye da kakanni, Afirka.

Masu amfani da kafar TikTok da suka yi arba da bidiyon sun matukar yabawa da man kadanyan. Wasu su na tambayar yadda za su samu.

Mai amfani da @uncoveredbeauty__ ce ta wallafa a dandalin TikTok.

Martanin 'yan soshiyal midiya

@Freya Lady ta yi tambaya:

"Ta ya zan same shi.?"

@M Stevens ya ce:

"Abun takaici shi ne mutane da dama ba su san komai game da man kadanyan gabashin Afirka ba daga Uganda da Sudan. Yafi taushi (wanda yafi sinadarin olein)."

Kara karanta wannan

Yadda Dalibi Ya Mayar Da Dakin Kwanansa Na Makaranta Ya Zama Karamin Kanti, Yana Ciniki Sosai

@kanazoe aliah ta yi tsokaci:

"Man kadanyan da yafi kyau shi ne na Burkina Faso, yafi arha kuma suna da man kadanya mai kyau har ma da 'ya'yan itace!!"

@Lynn Achieng183 ta ce:

"A baya nayi amfani man kadanyan yammacin Afirka da na Uganda. Ban san me suke sawa a na Uganda ba saboda bashi da kyau."

Da kudin makaranta, budurwa ta kafa kasuwanci da ya bunkasa

A wani labari na daban, wata budurwa ta kafa kasuwancin abinci da kudin makarantar ta yayin da ta ke daliba.

A yanzu da ta kammala karatu, kasuwancin ya bunkasa kuma ta mayar da hankalinta kacokan a kansa tare da bayyana duniya abinda ta ke.

Asali: Legit.ng

Online view pixel