Bidiyon Tsohon da Ya Bai yi Bacci ba Tun 1962 ya Ba Jama’a Mamaki

Bidiyon Tsohon da Ya Bai yi Bacci ba Tun 1962 ya Ba Jama’a Mamaki

  • Bidiyon wani mutum wanda ya ce bai yi bacci ba ko sau daya tun daga shekarar 1962 ya yadu a yanar gizo kuma ya ba jama’a mamaki
  • Bidiyon da wani fitaccen ma’abocin amfani da YouTube ya wallafa mai suna Drew Binsky, wanda ya je har Vietnam don ganawa da mutumin da baya bacci
  • Bidiyon ya janyo martani masu bada mamaki masu tarin yawa inda wasu jama’a ke tantama idan da gaske ne baya baccin

Wani mutum ‘Dan asalin kasar Vietnam wanda ke ikirarin bai taba bacci ba tun daga shekarar 1962 ya yadu a wani bidiyo da ya bayyana a yanar gizo.

Tsohon da baya bacci
Bidiyon Tsohon da Ya Bai yi Bacci ba Tun 1962 ya Ba Jama’a Mamaki. Hoto daga Instagram/@drewbinsky
Asali: Instagram

Mutumin mai suna Thai Ngoc yace ya kwashe shekaru 61 ba tare da ya rufe idanuwansa da sunan hutawa don yin bacci ba.

Wani fitaccen ma’abocin amfani da YouTube mai suna Drew Binsky ne ya wallafa bidiyon a Instagram bayan takakkiyar da yayi don ganawa da mutumin har kasar Vietnam.

Kara karanta wannan

Dalla-dalla: An gano sunayen makiyaya 37 da jirgin sojin sama ya babbaka a jihar Arewa

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Sadu da Thai Ngoc wanda bai taba bacci ba tun 1962

A bidiyon, an ga mutumin yana shan sigari kuma idanuwansa biyu bude duk da kuwa kwance yake a kasa.

Jama’a da dama a Instagram sun ce da tuni mutumin ya mutu idan bai yi bacci ba na wannan tsawon lokacin.

Wasu kuwa cewa suka yi jikin ‘dan Adam ba zai iya jure wannan tsawon shekarun ba ba tare da yayi bacci ba.

Wanne lokaci ‘Dan Adam zai iya dauka babu bacci?

Kamar yadda Healthline, wata shafin yanar gizo mai bayanai kan kiwon lafiya ya bayyana, mutum na iya fara surkulle da gane-gane idan ya dauka dogon lokaci babu bacci.

Yace:

“Mafi dogon lokacin da aka taba dauka babu bacci shi ne sa’o’i 264 ko kwanaki 11 a jere. Duk da babu tabbacin tsawon lokacin da ‘dan Adam zai iya kwashewa babu bacci, babu dadewa illar rashin baccin ya ke fara nunawa.”

Kara karanta wannan

Sakamakon Zaben 2023: A Karshe Babban Sarkin Yarbawa Ya Magantu Kan Soke Zabe Da Obasanjo Ya Ce A Yi

Kalla bidiyon a kasa:

Martani daga ma’abota amfani da Instagram

@livefreemayra yace:

“Idan da ace baya bacci, mutuwa zai yi. Ba zai yuwu ba. Ba tare da ya sani ba, yana bacci ko na mintuna 30 ne. Jikin mu ba Haka yake aiki ba.”

@downtotravelling yace:

“Ta yuwu dalibin injiniyanci ne”

Miji nagari: Magidanci ya siyawa matarsa adaidaita Sahu 2

A wani labari na daban, wani magidanci ya gwangwaje matarsa da kyautar adaidaita sahu 2 ranar zagayowar haihuwan ta.

Cike da farin ciki da annashuwa Matar ta dinga kuma inda daga bisani ta zage tana daukar hoto da kyautukan.

Asali: Legit.ng

Online view pixel