Kotu ta Umarci Budurwa ta Biya Saurayi N1m Bayan Karbe Masa Kudade kuma ta ki Aurensa

Kotu ta Umarci Budurwa ta Biya Saurayi N1m Bayan Karbe Masa Kudade kuma ta ki Aurensa

  • Alake Richard Timwine da Fortunate Kyarikunda sun fada kogin soyayya a shekarar 2015 inda suka fara ganin juna da zummar shigewa daga ciki
  • Timwine, wanda ke koyarwa a makarantar Firamare, ya bayyana wa kotu yadda ya dauki nauyin Kyarikunda da kudinsa
  • Daga karshe, Kyarikunda ta murje ido ta ki auren Tumwine, hakan yasa ya makata a kotu inda aka umarceta da ta biyashi sama da 1miliyan

Wata kotu a Uganda ta umarci wata mata a yankin Kanungu da ta biya tsohon sauranyinta sama da N1 miliyan a matsayin diyyar kin aurensa da tayi.

Soyayya
Kotu ta Umarci Budurwa ta Biya Saurayi N1m Bayan Karbe Masa Kudade kuma ta ki Aurensa. Hoto daga dailynigerian.com
Asali: UGC

Richard da Fortunate sun fara soyayya a shekarar 2015

Kamar yadda takardun kotun da Legit.ng ta gani da shafin Twitter Ivan Bwowe, Richard Timwine da Fortunate Kyarikunda sun fada kogin soyayya a 2015, har suka kai ga alkawarin aure a 2018.

Kara karanta wannan

Fasto Ya Yada Labarin Karya Cewa Ya Mutu Gudun Kada Ya Biya Bashin N3m

Tumwine, wanda malamin makarantar Firamare ne, ya shaidawa kotu yadda ya dauki ragamar rayuwar Kyarikunda wanda ya hada da daukar nauyin karatun dufulomarta a fannin shari'a da cibiyar cigaban shari'a (LDC).

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Haka zalika, ya bayyanawa kotu yadda ya kashe ma ta sama da N1 miliyan.

Kamar yadda kotun Majistare ta Asanasia Mukai ta bayyana, Kyarikunda ba ta cika alkawarin auren ba, saboda haka, abun ya matukar gigita saurayin nata.

Wandan shi ne ya sa ya ke da alhakanin ta mayar masa da kudinsa da ya kashe ma ta. Har ila yau, Mukobi ta umarci Kyarikunda da ta biya Tumwine N125,000 na barnar da tayi masa, rashin kwanciyar hankali da ta jefa shi, gami da zamba cikin aminci.

Sannan an umarci Kyarikunda da ta biya duk kudin da tsohon saurayin nata ya kashe a shari'ar.

Kara karanta wannan

Assha: Dan takarar majalisa a jam'iyyar su Kwankwaso a Arewa ya sace N681m daga asusun banki

"Don tabbatar da lamarin, shedar tura kudaden da mai kara ya yima wacce ya ke kara sun bayyana wayar mai kara da sunan Richard Tumwine zuwa wayar wacce ake kara da sunan Fortunate Kyarikunda."

- Kotun majistare ta lura da hakan.

An shaidawa kotu yadda Kyarikunda ta yi watsi da Tumwine ta hanyar cewa iyayenta basa so ta auri tsoho.

"Wannan ba hujja ba ce, mummunar fassara ce kuma zamba ne. A kowanne yanayi, wacce ake karar na da damar kin amincewa da kokon barar soyayyar mai korafin da farko don gidan daukar nauyinta."

- A cewarsa.

"Wannan ba hujja ba ce, mummunar fassara ce kuma zamba ne. A kowanne yanayi, wacce ake karar na da damar kin amincewa da kokon barar soyayyar mai korafin da farko don gidan daukar nauyinta."

- A umarninta.

Malam biyu sun shirya bikin gabatarwa a watan Fabrairu, 2022 amma hakan bai faru ba kuma babu wani kwakkwaran bayani.

Kara karanta wannan

Soyayya Gamon Jini: Dirarriyar Matar Aure ta Bayyana Wadan Mijinta a Bidiyo, Tace Suna Cikin Farin Ciki

Matar Aure ta kama mijinta a wurin cin abinci da budurwa, ta tayar da hazo

A wani labari na daban, wata matar aure ta tayar da hazo a wurin wani cin abinci da ta kama mijinta tare da budurwa.

An dinga kokarin kwantar mata da hankali amma lamarin ya ci tura, ta ki hakuri su koma gida kafin baje-kolin takaicinta.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng

Online view pixel