Bidiyo: Magidanci 'Dan Najerya ya Gwangwaje Matarsa da Kyautar Adaidaita Sahu 2 Ranar Bazday Dinta

Bidiyo: Magidanci 'Dan Najerya ya Gwangwaje Matarsa da Kyautar Adaidaita Sahu 2 Ranar Bazday Dinta

  • Mijin wata mata ya mata kyautar ba-zata ranar zagayowar haihuwarta wanda ya narkar da zukatan jama'a
  • Baya ga kudin, fulawa da waya da ya ba ta, mutumin ya siya wa matar tasa keke napep biyu don tayi kasuwanci
  • Mutane da dama a shafin tsokaci sun ce ya cika 'dan halas yayin da suka yaba da kaifin basirar da ta biyo bayan kyautar

Wani mutumi 'dan Najeriya ya zama abun kafa misali kan yadda ya dace maza su nuna kauna ga matansu ranar zagayowar haihuwarsu.

Mata da miji
Bidiyo: Magidanci 'Dan Najerya ya Gwangwaje Matarsa da Kyautar Adaidaita Sahu 2 Ranar Bazday Dinta. Hoto daga TikTok/@nesta_surprise8
Asali: UGC

Wani bidiyo da @nesta_surprise8 ta wallafa ya nuna lokacin da mata ta kasa daina kukan farin cikin yadda mijinta ya yi amfani da N500,000 don gina ma ta ginin kudi.

Ya hada ma ta fulawa da wata N200,000. Matar ta tsunduma cikin farin ciki game da keke napep din da ya siya maya yayin da ta dauki hotuna dasu.

Kara karanta wannan

Karin Bayani: "Ba Zan Yarda Ba" Peter Obi Ya Maida Martani Mai Dumi Kan Nasarar Tinubu

Ya bata kyautar adaidaita 2 don sana'a

Don tabbatar da matar ta samu wata hanyar samun sulalla, mutumin ya siyo ma ta sabbin adaidaita sahu biyu. Ya kara ma ta da waya kirar Iphone 14 da agogon Lu'u-lu'u don ya dace da kyautar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Matar ta dauki hotuna da sabbin adaidaita sahu biyu, inda mutane da dama a shafin tsokacin wallafar suka lakabawa mijin sunan mijin da yafi kowanne nuna kauna a shekarar.

Daga lokacin da aka tattara wannan rahoton, bidiyon ya janyo sama da tsokaci 2,000 da sama da jinjina 90,000.

Jama'a sun yi martani

Legit.ng ta tattaro wasu daga cikin tsokacin kamar haka:

elikachunga23 ta ce:

"Zan cigaba da tafa maka har sai har sai yazo kaina, ina taya ki murna."

Martha unusual ta ce:

"Na yaba da dabarar siyan keken saboda wannan hanyar samun kudi ce duk karshen mako."

Kara karanta wannan

Sakamakon Zaben 2023: A Karshe Babban Sarkin Yarbawa Ya Magantu Kan Soke Zabe Da Obasanjo Ya Ce A Yi

dotunmide ya ce:

"Kyautar keken hannun jari ne gareta. Mutumin ya yi kokarin."

Anni gold ta ce:

"Tabbas ya cika dan halas da ya hado da keke napep."

Ada Bekee ta ce:

"Inyamurai ne kadai zasu fahimci amfanin keken... saboda mune kadai muke da dabarar kasuwanci... wadanda ke tambaya meye amfanin keken... baku da hankali."

Matashi ya je wurin biki da akwatin kudi, ya dinga wurga bandira

A wani labari na daban, wani 'dan Najeriya ya bar jama'a baki bude bayan zuwansa wurin wani biki da akwati makare da sabbin kudi.

Ya dinga wurgawa amarya da ango bandiran sabbin kudin a matsayin likin da yake musu wurin bikin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel