Bidiyon 'dan Najeriya Ya Je Biki da Akwatin Kudi, Yana ta Watsa Bandir Din Sabbin Takardun Naira

Bidiyon 'dan Najeriya Ya Je Biki da Akwatin Kudi, Yana ta Watsa Bandir Din Sabbin Takardun Naira

  • Bidiyon wurin wani shagalin biki ya janyo cece-kuce a dandalin Instagram bayan wani mutum ya bayyana yana watsa bandiran takardun sabbin kudi
  • Amarya da ango dai suna zaune a mazauninsu yayin da mutumin ya bayyana dauke da akwatin kudin da alamu ke nuna dankare suke da sabbin Naira
  • Ya dinga wurga bandir bayan bandir ga amarya da ango, amma ma'abota amfani da Instagram ba su sassauta masa ba wurin sharhinsu

Wani 'dan Najerya ya yadu a bidiyo a Instagram bayan ya dinga wurga bandiran sabbin takardun Naira ga wasu amarya da ango.

Amaryar da angon na zaune kuma ba rawa suke ba yayin da mutumin ya bayyana a wurin bikin dauke da akwatin kudi.

Amarya da ango
Bidiyon 'dan Najeriya Ya Je Biki da Akwatin Kudi, Yana ta Watsa Bandir Din Sabbin Takardun Naira. Hoto daga Instagram/@bcrworldwide.
Asali: Instagram

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Kara karanta wannan

Daga Ganinta na San na Samu Abokiyar Rayuwa: Bakar Fata Ya Nemi Baturiya ta Aure shi Bayan Kwana 4 da Haduwa

Wani hadiminsa ya riko masa akwatin kudin kuma ya bude inda sabbin kudin suka bayyana dal.

Mutumin yayi yayyafin kudi kan ango da amarya

Ya dinga watsa bandir bayan bandir na kudin ga amarya da angon wadanda ke zaune suna kallonsa ba tare da sun ce komai ba kan abinda yake yi.

Wasu ma'abota amfani da kafar sada zumunta ta Instagram sun matukar harzuka da yadda ya ke watsa kudin ga ma'auratan inda suka ce babu mutuntawa a lamarin.

Sauran sun ce mutumin kawai yana ta watsi da takardun sabbin Naira duk da kuwa rashinsu a gari da ake yi. @bcrentertainment ne suka wallafa bidiyon a shafinsu na Instagram.

Jama'a sun yi masa martani

@anneyjim yace:

"Girman kai ya kashe daya."

@__wendyrose tayi martani da:

"Abubuwa na faruwa."

@joshchamp_ yayi tsokaci da:

"Babu mutuntawa gaskiya."

@magicman_010 yace:

"Wanne irin rashin mutuntawa ne ku mata ba za ku lamunta ba saboda kudi? Shiyasa bai dace maza su dauke ku da muhimmanci ba. Duk da dai ku kuka ce, naushi mace a ido kuma ka siya mata mota."

Kara karanta wannan

Bidiyo: Leburori Sun yi Sama da Abokin Aikinsu, Duk a Cikin Murnar Cin Jarabawa da Yayi

@chizzyfrancis4 yace:

"Ban damu da kudi ba amma me zai sa ka zo bikina kana wurga kudi a kai na?"

Budurwa ta lamushe kudin saurayi ta ki aurensa, ya maka ta a kotu

A wani labari na daban, wata budurwa ta ci kudin saurayi da alkawarin cewa za su yi aure amma daga baya ta fasa auren.

Sai dai matashin ya maka ta a kotu inda alkali ya bayyana cewa sai ta biya shi diyyar N1 miliyan na cin amana.

Asali: Legit.ng

Online view pixel