Hukumar Zabe ta Kara Wa’adin Rufe Karbar PVC a Fadin Najeriya

Hukumar Zabe ta Kara Wa’adin Rufe Karbar PVC a Fadin Najeriya

Hukumar zabe mai zaman kanta ta INEC ta tsawaita wa’adin daina karbar katin zabe na dindindin zuwa ranar 5 ga watan Fabrairun 2023, Channels Tv ta rahoto.

Katikan zabe
Hukumar Zabe ta Kara Wa’adin Rufe Karbar PVC a Fadin Najeriya. Hoto daga channelstv.com
Asali: UGC

INEC ta tsayar da ranar 31 ga watan Janairu matsayin ranar da za a daina karbar katin zaben dindindin amma kwamishinan hukumar, Festus Okoye yace an tsawaita tare da kara wa’adin don baiwa ‘yan Najeriya damar karbar katikansu.

Karin bayani na tafe…

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng