Cike da Alfahari, 'Dan Najeriya ya Ciccibi Janaretonsa har Gidan Mai, Ya Siya Fetur a Bidiyo

Cike da Alfahari, 'Dan Najeriya ya Ciccibi Janaretonsa har Gidan Mai, Ya Siya Fetur a Bidiyo

  • Bidiyon wani matashi wanda ya bayyana a wani gidan mai don siyan fetur da 'dan karamin janaretonsa ya yadu a dandalin TikTok
  • A wani faifan bidiyo, an ga mutumin cike da alfahari yana kallon yadda mai bada man ke zuba masa a tankin janareton
  • Dabi'unsa da karamin janareton ya bar wasu mutune baki bude cike da mamakin yadda bai je da wani abun zubawa ba

Martani masu ban dariya sun taru karkashin wani bidiyon TikTok na wani mutumi da yaje gidan mai da 'dan karamin janaretonsa.

Mai Janareto
Cike da Alfahari, 'Dan Najeriya ya Ciccibi Janaretonsa har Gidan Mai, Ya Siya Fetur a Bidiyo. Hoto daga TikTok/@twelve_twenty1
Asali: UGC

A bidiyon da yayi yawo, an ga yadda mutumin dauke da wani janareto da aka fi sani da 'burin talaka' inda ya mayar da hankali wajen siyan mai.

Bidiyon ya fara ne da nuna lokacin da mai bada mai ke zuba masa man fetur tare da jansa da hira cikin nishadi.

Kara karanta wannan

Soyayya Ta Gaskiya: Bidiyon Wani Bature da Matarsa Bakar Fata Da Suka Shafe Shekaru 45 da Aure Ya Yadu

Hirarsu a bidiyon ba ta fito sosai ba, amma masu amfani da kafar TikTok suna cigaba da duba bidiyon. Da yawansu sun nuna alamun mamaki da dariya a sashin tsokaci.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Wasu sun yi mamakin dalilin da yasa mutumin bai je da jarka gidan man ba don siyan man amma ya zabi daddakar janareton.

Sai dai, wasu suna ganin ba wani abu bane idan mutumin yayi haka.

Mai amfani da @twelve_twenty1. ne ya wallafa bidiyon a dandalin TikTok din, wanda mutane da dama suka nishadantu, wasu kuma suka cika da mamakin yadda ya dauki janareton a matsayin wani kayan gabas.

Kalla bidiyon:

Amarya tace ga garinku kwanaki 11 bayan aure

A wani labari na daban, cike da kuna tare da alhini wani sabon ango ya sanar da mutuwar matarsa bayan kwanaki 11 da suka angwance.

Kara karanta wannan

Bidiyon Baturiya Tana Yawo a Hargitse Babu Takalmi a Lagas Ya Girgiza Intanet, Bidiyon Ya Yadu

A wallafar da yayi tare da kyawawan hotunan amaryarsa wacce yanzu ta zama marigayiya, ta sha alkyabba inda ta dauka kyau yayin da ya sha nadi cike da da nuna al'adar Hausawa.

Ba na ayyukan ashsha, matashi da ya gin katafaren gida

A wani labari na daban, wani matashi 'dan Najeriya ya bayyana irin gidan alfarmar da ya tamfatsa amma ya sanar da sirrin wannan nasarar.

A cewarsa, ba ya shaye-shaye, ba ya neman matan banza, ba ya yawon dare, wadannan suna daga cikin sirrin nasararsa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel