Bana Shaye-shaye: Matashi ya Tamfatsa Gidan Alfarma, Ya Bayyana Yadda Ya Samu Nasarar a Bidiyo

Bana Shaye-shaye: Matashi ya Tamfatsa Gidan Alfarma, Ya Bayyana Yadda Ya Samu Nasarar a Bidiyo

  • Wani mutumi 'dan Najeriya ya tafi dandalin soshiyal midiya yana mai bayyana katafaren gidansa da jan tayis dinsa da kamfacecen haraba
  • Mai gidan cike da alfahari ya bayyana irin munanan abubuwan da ya kauracewa har ya kai ga samun wannan babbar nasarar
  • Wasu masu amfani da yanar gizo sun kyamaci munanan dabi'un da mutumin ya jero, inda suka bukaci ya bayyana yadda ake samun kudi

Wani mutumi 'dan Najeriya ya janyo cece-kuce bayan bayyana katafaren gidansa.

A bidiyon TikTok din da ya wallafa da daddare gami da nuna gidan daga kofar gaba zuwa harabar.

Katafaren Gida
Bana Shaye-shaye: Matashi ya Tamfatsa Gidan Alfarma, Ya Bayyana Yadda Ya Samu Nasarar a Bidiyo. Hoto daga TikTok/@officialafro_g
Asali: UGC

Mamallakin katafaren gidan ya bayyana wasu dalilai da suka kaisa ga nasara, wanda hakan ya janyo cece-kuce.

Mutumin ya lissafo wasu abubuwa da ya nisanta kafin samun gina wannan aljannar duniyan.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kara karanta wannan

Haren-haren da ake kaiwa cikin daji mata da yaran Fulani kawai ake kashewa, Gumi

Kamar yadda mutumin ya rubuta kan faifan bidiyon:

"Na samu wannan nasarar ne saboda ba na busar hayaki. Ba na zuwa gidan casu. Ba na shan giya. Kuma ba na bin mata."

A wani faifan bidiyo da ya gabata, mutumin ya labarta yadda aka yi garkuwa da mahaifinsa a 2010 sakamakon hassadar da ake masa.

Sai dai matashin biloniyan ya ce "mahaifinsa ya dawo" ta hanyarsa.

Martanin 'yan soshiyal midiya

Don's Ernest ya ce:

"Kai oga ka bar wadannan abubuwan idan Ubangiji ya so sanya maka albarka tabbas zai sanya maka albarka."

Mercyderah ta ce:

"Wannan filin ya hadu, ya kusa zama katafaren gidaje biyu ina taya ka murna. Na shafi tabaraki."

Slimzy Iheanyichukwu ya ce:

"Nima ba na yin duk wadannan abubuwan amma har yanzu ina fama da kebura."

Ofysa_yannie ya ce:

"Ina taya ka murna yallabai, hakan za ifi idan ka auri mace ta gari, sh ine za ka kai ga nasarar duk wadannan abubuwan, idan ta baka natsuwar rai."

Kara karanta wannan

Haihuwa Mai Rana: Matashi Dan Najeriya Ya Dankarawa Iyayensa Gida a Kauye, Bidiyon Ya Yadu

Ebuka Ibezim ya ce:

"To hakan na nufin duk wadannan ke yin irin abubuwan da ka lissafo ba za su yi nasara ba?

Promiseachor6 ya ce:

"'Yan shaye-shaye sunfi samun nasarori kada ka zo nan ka lakaba mana suna mu ji kamar bama da amfani."

Matar aure ta fatattaki 'dan da ya gwnagwaje ta da mota sabuwa

A wani labari na daban, wata matar aure ta kori 'dan ta bayan ya bata kyautar sabuwar motar ranar bikin zagayowar haihuwarta.

Matar auren cike da fushi ta bayyana cewa 'danta dalibi ne kuma a ina ya samo irin wannan kudin idan ba damfara ya fara ba?

Asali: Legit.ng

Online view pixel