Kyakyawar Baturiya Ta Tafi Da Saurayinta Dan Najeriya Kasarsu Don Ya Gana Da Danginta, Bidiyon Ya Kayatar

Kyakyawar Baturiya Ta Tafi Da Saurayinta Dan Najeriya Kasarsu Don Ya Gana Da Danginta, Bidiyon Ya Kayatar

  • Wata baturiya ta wallafa bidiyo a intanet tana nuna wa mutane yadda ta tafi da masoyinta dan Najeriya kasarsu don gabatar da shi ga yan uwanta lokacin kirsimeti
  • Kyakyawan budurwar ta tabbatar saurayin nata ya saki jiki kuma ya ci abinci tare da danginta
  • Mutane da dama sun yi tsokaci kan bidiyon masoyan, wasu na cewa mutumin ya yi sa'a kuma suka ce ta kula da shi

Wata mata farar fata ta wallafa wani bidiyo da ke nuna lokacin da ta kai saurayinta dan Najeriya kasarsu domin ya gana da yan uwanta a lokacin kirsimeti.

Matar yar kasar Poland duk da cewa ta san saurayinta ya yi nisa da kasarsa, tana son rage masa kewa ya ji 'tamkar gida' ya ke.

Saurayi da budurwa
Bidiyon Kyakyawar Baturiya Da Ta Tafi Da Saurayinta Dan Najeriya Kasarsu, Ta Gabatar Da Shi Wurin Yan Uwanta. Hoto: Photo source: TikTok/@samuelandlena
Asali: UGC

Budurwa ta kula da saurayinta

A bidiyon da dubban mutane suka yi ta tsokaci a kai, budurwar ta nuna wa duniya saurayinta. Bayan jera abinci, dukkan yan uwanta sun zauna a tebur, suka ci abinci tare.

Kara karanta wannan

Sabon Salo: Wata Amarya Ta Yi Amfani da Maza 5 a Matsayin Kawayenta Ranar Biki, Bidiyon Ya Ja Hankali

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Yayin da yan uwanta suke tattaunawa da matashin, suna sauraron wakar Burna Boy a talabijin.

Kalli bidiyon a kasa:

A lokacin da aka hada wannan rahoton, a kalla mutane 500 sun yi tsokaci kan bidiyon sannan mutum 19,000 sun latsa like.

Legit.ng ta tattara wasu daga cikin martanin da wasu suka yi:

Kai ya ce:

"Idan ni ne sai na tambaya a ina lewandoski ya ke zaune."

DeamieanKemet ya ce:

"Wannan mutumin jarumi ne."

osmondamu ya ce:

"Irin wannan budurwar mutum ke bukata. Dan uwa na ka yi sana'a."

Alexei Aleksandra ta ce:

"Da fatan kin ji dadin kirsimeti da yan uwanki."

Nathan Onyeka ya ce:

"Mun gode bisa kula da shi da kika yi ... duniya ga Najeriya."

Big Bear ya ce:

"Don Allah ki kula da yaro na."

seanna4 ya ce:

Kara karanta wannan

Ya Yi Sa’a: Matashiyar Baturiya Ta Kai Saurayinta Dan Najeriya Gida Don Iyaye Su Gani, Ta Rangada Masa Girki

"Dan uwa na kana son cin cheese da bacon? Gara ka ci Eba da miya."

femme_moon ya ce:

"Matar mu kyakyawa ce."

Asali: Legit.ng

Online view pixel