Bidiyon Yadda Wata Kyakkyawar Budurwa Ta Gaya Wa Dan Acaba 'Ina Son Ka'

Bidiyon Yadda Wata Kyakkyawar Budurwa Ta Gaya Wa Dan Acaba 'Ina Son Ka'

  • Wata kyakkyawa kuma dirarriyar budurwa ta yi wasa da wani ɗan Acaɓa bayan sun haɗu
  • Ita ta fara buga wasan, inda ta bayyana masa sirrin zuciyarta kana ta ja hankalinsa duk da yana jin kunya
  • Bayan komai ya kankama budurwa ta ba shi kyautar kuɗi, lamarin da ɗan Okadan ya ji daɗinsa a wani Bidiyo

Wata budurwa yar Najeriya ta haddasa cece-kuce a Soshiyal midiya bayan ta bayyana wa wani ɗan Acaba rassan ƙaunar da ya kafa a zuciyarta.

A wani bidiyo da aka wallafa a shafin TikTok ya nuna yadda budurwar ta ja Ɗan Acaban da hira duk da yana jin kunya daga bisani ta zayyana masa cewa ya tafi da imaninta.

So gamon jini.
Bidiyon Yadda Wata Kyakkyawar Budurwa Ta Gaya Wa Dan Acaba 'Ina Son Ka' Hoto: @annie_khalie29
Asali: UGC

Mutumin wanda ya nuna kunya ya kawar da kansa ya yin da ta shafa masa kai, ta roke shi ya taimaka ya karɓe ta, ya gaya mata shi ma yana kaunarta.

Kara karanta wannan

"Ka Biyo Ni": Wata Dirarriyar Budurwa Ta Nemi Ɗan Acaba Ya Kwanta da Ita, Bidiyon Ya Girgiza Mutane

Yayin da ya saduda da bukatarta, Ɗan Acaban ya faɗa mata yana sonta daga nan kuma sai ta ba shi kyautar N20.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Ya sa hannu ya amsa cikin hamdala yayin da dirarriyar budurwar ta kama hanya ta bar wurin.

Jama'a sun bayyana ra'ayoyinsu

Drey ya ce:

"Wata rana wani sai ya yi amfani dake wajen buga kalar wannan wasan."

Korez 1 ya ce:

"Wai abinda nake gani ta ba shi N20 ce ko me? A dawo da bako ya sha kwai nawa ake hawa Babur ne."

Lattojnr12 ya ce:

"Mutumin fa zai je ya gaya wa dukkan abokansa abinda ya faru amma ba zasu yarda ba, ina ganin sai ya yi mafarkin wannan."

Onyeka XD yace:

"Abun tausayi an yi wasa da hankalin ɗan uwa."

Kecho Man yace:

"Idan da namiji ne ya yi wa wata mace haka, da yanzu abun ya zama matsala."

Kara karanta wannan

Ba Girman Kai: Zankadeɗiyar Budurwa Mai Digiri Ta Bude Wurin Wankin Mota, Bidiyonta Ya Ƙayatar da Mutane

Kwana Hudu da Aure, Amarya Ta Kama Angonta da Yar Uwarta Suna Jin Dadi a Gado

A wani labarin kuma Amarya Ta shiga yanayi bayan ta kama Angonta ya kwanta da yar uwarta a kan gadonsu, Abun ya ja hankalin mutane

Wata sabuwar amarya ta gamu da jarabawa kwana hudu kacal da ɗaura mata aure da wanda take ƙauna, bisa tilas ta kauracewa gidan aurenta don ta huta.

Amaryar ta gane wa idonta cin amanar da Angonta ke yi abun bakin cikin kuma tare da yar uwarta kuma akan gadonsu na aure.

Asali: Legit.ng

Online view pixel