Saurayin da Aka yi wa Budurwa Baiko dashi, Ya Bukaci ta Biya N2.2m na Kudin Zoben da ya Bata

Saurayin da Aka yi wa Budurwa Baiko dashi, Ya Bukaci ta Biya N2.2m na Kudin Zoben da ya Bata

  • Wani mutumi ya tada 'kura a soshiyal midiya bayan ya bukaci matar da zai aura ta maido masa wani bangaren kudin da ya siya mata zobe
  • Mutumin ya nuna bukatar hakan ne bayan sanya ranar aurensu da matar ta hanyar sanya mata zobe mai kimanin N2.2 miliyan
  • A cewarsa, dole ne matar ta biya wani bangaren kudin zoben wanda a kalla zai kai kusan N1.1 miliyan ne

Wani mutumi yayi yawo a yanar gizo bayan ya sanyawa budurwarsa zoben sa rana gami da bukatar ta biya kudin zobe mai tsadar da aka yi amfani da shi.

Budurwa da saurayi
Saurayin da Aka yi wa Budurwa Baiko dashi, Ya Bukaci ta Biya N2.2m na Kudin Zoben da ya Bata. Hoto daga Dragana991 and Burazin/ Getty Images
Asali: Getty Images

Mutumin ya siya zoben kan N2.2 miliyan, yayin da ya shigar da bukatar aurensa gareta ita kuma ta amince. Mutumin ya tsaya kan bakar dole budurwarsa ta biya wani bangare daga cikin N2.2 miliyan na zoben.

Kara karanta wannan

Dirama, Wani Dan Kasuwa Ya Hargitse a Kotun Musulunci Kaduna, Yace Yana Kaunar Matarsa

Matar tayi matukar shan mamaki da bukatar da mutumin ya shigar saboda kamar yadda mutane da dama suke zaton mutumin ke da alhakin biyan kudin zoben shigar da bukatar auren.

Idan har matar za ta biya rabin kudin, za ta biya mutumin N1.1 miliyan.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kamar yadda labarin ya nuna, mutumin ya shaidawa matar cewa, tunda dukkansu matsayi daya suke da shi a soyyayar, ya kamata su biyun su biya kudin zoben.

Masoyan biyu sun dade suna daukar ragamar abubuwan da ya shafesu duk da kayayyakin abinci.

Alaka tsakanin masoyan ta lalace tun daga faruwar lamarin.

Southern China Morning Post ta ruwaito yadda lamarin ya auku a Taiwan.

Martanin jama'a

Wani mai amfani da yanar gizo ya rubuta:

"Daga yanzu, za ki dinga wanke rabin bayin shi kuma ya wanke rabi."

Kara karanta wannan

Bidiyon Yadda aka Tarwatsa Bikin Aure Kan Maggi da Kiret din Maltina da Dangin Miji Basu Kai Wurin Daurin Aure ba

Wani yayi tsokaci:

"Ki mayar masa da zoben gami da fatattakarsa."

Bidiyon budurwa tana yi wa saurayi sata, ya kama ta

A wani labari na daban, wani matashi ya fara zargin budurwarsa tana masa halayyar bera amma bai riga ya tabbatar da hakan ba sai ya saka mata tarko.

Ya tarkata kayan wankinsa inda ya zuba kudade a ciki amma budurwar na budewa ta gani tayi wuff ta boye su.

Ko bayan da saurayin ya kama ta, tayi mirsisi tare da murje idonta inda ta nuna ba sata tayi ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel