Bidiyo: Shagalin Aure ya Tarwatse Saboda Ba a Hado da Maggi Tare da Sadaki ba

Bidiyo: Shagalin Aure ya Tarwatse Saboda Ba a Hado da Maggi Tare da Sadaki ba

  • Wata hatsaniya da rikici ya barke a wajen shagalin biki yayin da aka gaza gudanar da bikin a lokacin saboda wasu matsaloli
  • Mutumin da aka biya don yin bidiyon bikin ya ya bayyana yadda bikin ya watse saboda dunkulen 'dan'dano da kiret biyu na maltina
  • A cewarsa, mutanen ba su ji dadi ba saboda wadannan abubuwan basa cikin kudin sadakin auren, hakan yasa suka ki badawa

Wani bikin Najeriya na al'ada ya tarwatse saboda dunkulen 'dan'dano da kiret biyu na lemo saboda baya cikin sadakin aure.

Bikin gargajiya
Bidiyo: Shagalin Aure ya Tarwatse Saboda Ba a Hado da Maggi Tare da Sadaki ba. Hoto daga TikTok/@loloskitchen13
Asali: UGC

Wani bidiyon TikTok da aka dauka daga wurin bikin ya bayyana yadda aka tsara abubuwa amma mutane suka tarwatsa.

Wani mutumi da ya bada rahoto game da bikin ya bayyana yadda aka biya shi don yin bidiyon bikin amma hakan bai yuwu ba yayin da ya watse.

Kara karanta wannan

Bidiyo: Dumu-dumu Saurayi Ya Kama Budurwarsa Tana Masa Sata, Tayi Borin Kunya Kiri-kiri

A cewersa, ya kamata amaryar ta bayyana gaban mutane sau uku amma hatsaniyar ta barke kafin bayyanarta karo na farko.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Dangin amaryar sun tsaya a kan cewa ba za su amince da abun da aka basu ba saboda babu dunkulen 'dan'dano da kiret biyu na maltina a kayan sadakin amaryar. Sun zargi dangin angon da yin awon gaba da kayayyakin.

Kamar yadda ganau din ya shaida, angon ne ya ce ba sai sun bada ba.

Martanin jama'a

chioma peace ta ce:

"Idan da nice kawai zan tura musu da kudin, ba na son irin wadannan shirmen, ba su isa su kira ni suce min kudin bai isa ba, ba za su iya kirana ba su ce min kudin ba za su isa ba, idan suka tambayi 20 a basu 10."

benny_b221 ta ce:

Kara karanta wannan

Bidiyon Matar Aure Tana Gaggawar Ba Miji Abinci a Baki Kada ya Makara Aiki ya Janyo Cece-kuce

"Kai wadannan kadangarun bakin tulu ne, yawancin matan dake wurin, 'ya'yansu sun haifi shegu bakwai-bakwai a gidan ubansu ba tare da aure ba."

Teddybear1 ta ce:

"Lallai zan iya alakanta shi, sun so yin haka ga 'yar uwata, muka rufesu wajen kofar, dukkansu sun fara cece-kuce wai za su yi magana a kan abun. Mugayen mutane."

swatty ta ce:

"Idan da gaske suna kaunar kansu ya kamata su bar mutane su shiga a yi bikin tare da dangin mijin."

Eyshaoo ta ce:

"Ina batun shinkafar biki saboda mutane sun kona mai sun zo."

chijiokeblessing_ ta ce:

"Ya kamata ta basu idan ba haka ba za su lalata mata aure."

Testimony ta ce:

"Dole wadannan tsofaffin ne. Sun cika zakewa kamar su suka bada ajiyar kudin.."

Rabon fada yayi wa matashi sanadin hannu daya a Kano

A wani labari na daban, wani matashi mai suna Salisu Hussaini ya zama mai hannu daya bayan ya je rabon fada.

Daya daga cikin 'yan daban dake fadan ya nemi soka masa wuka a ciki amma ya kai hannunsa wanda dafin cuta ta shiga har sai da aka cire shi baki daya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel