Dubun Budurwa ya Cika, Saurayi Ya Kama Tana Sace Masa Kudinsa a Bidiyo

Dubun Budurwa ya Cika, Saurayi Ya Kama Tana Sace Masa Kudinsa a Bidiyo

  • Wani mutumi 'dan Najeriya ya hadawa budurwarsa tarko bayan zargin ta da daukar tsawon lokaci tana masa halin bera
  • Mutumin ya bar wasu kudade da gangar a tufafinsa gami da zura ido yayin da ta dauki kayan da sunan wankewa
  • Sai dai, budurwar da aka 'danawa tarkon ta fada amma ta nemi basarwa duk da yadda ya kamata dumu-dumu

Wani mutumi 'dan Najeriya ya wallafa wani bidiyon budurwarsa yayin da take satar masa sulalla, inda ta fake da wanke masa tufafi a waje.

A bidiyon da aka wallafa a dandalin TikTok, ya nuna lokacin da take bincike masa wani 'dan kamfansa, sannan daga bisani ta hanzarta boye kudin da ta gani a ciki.

Budurwa mai sata
Dubun Budurwa ya Cika, Saurayi Ya Kama Tana Sace Masa Kudinsa a Bidiyo. Hoto daga TikTok/@saskid_lae
Asali: UGC

Ba tayi zaton yana sanye da ido a kanta ba

Budurwar wacce ta duba hagu da dama kafin boye kudin ta matukar shan mamaki bayan ya kamata dumu-dumu.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

A lokacin da yayi ram da ita, matashin ya ce ya dade yana zargin ta da sace masa sulalla amma ta karyata hakan a baya.

Duk da titsiyen da aka mata, budurwar bata zamince da laifinta ba sai ma ta nemi kare kanta.

A cewarta, wannan kudin shi ne canjin sabulun da ta siya wanda aka yi amfani da shi wajen wanke masa tufafi.

Biyun sun yi rikici kwarai a bidiyon mai ban dariya, inda ta tada borin kunya gami da yin mursisi.

Tsokacin jama'a

mhiz Adegold ta ce:

"Naji dadin yadda tayi borin kunya bama tayi tunanin me za ta ce ba, oho dole dai ka biya kudin.. gwaji dai yayi gardama."

Obefemi Daniel ya ce:

"Dubi yadda tayi mursisi ta ki amsa laifinta har da masa borin kunya. Wannan kamar yadda mafarauci ya kama naman daji ne."

Ajala Nofisat969 ta ce:

"Lallai tsinuwa ta kusa fitowa daga bakin gayen, amma gashi ya hadiye kadama dai tayi amfani da abinci ta gama da shi."

@vedkiehorlar ta ce:

"Yadda take amfani da solo don ganin ko akwai sauran kudi a aljihun."

user841945412741 ta ce:

"Daidai ne idan ka bani kaya na wanke maka amma ba za ka aje kudi a aljihunka da kanka ba... kayanka zasu yi datti su gaji saboda kudinka ya dame ni."

@shinalowo ta ce:

"Ya aka yi ka tara duk wadannan kayan amma tawul kawai kake sawa. Haba.

Bidiyon gurgu mai kafa daya yan tuka keke da kwarewa

A wani labari na daban, wani bawan Allah ya dauka bidiyon wani gurgu mai kafa daya da ke tuka keke cike da gwaninta.

Ya kwararawa Ubangiji godiya kan baiwar lafiya da yayi masa da dukkan gabbai da ya mallaka.

Asali: Legit.ng

Online view pixel