Ikon Allah: Wani Mutumi Ya Sauya Fasalin Keke Napep Ta Koma Kamar Jirgin Helikwafta
- Wani Mutumi ya kayatar da mutane bayan ya sauya fasalin Keke Napep din da ya siya, ya maida ita abu mai ban sha'awa
- Mutumin mai basirar kirkira ya wallafa yadda Keken ta koma mai wutsiya kamar ta jirgin sama
- Masu amfani da kafafen sada zumunta da suka ga bidiyon sun yaba wa basirar mutumin
Wani mutumi ya wallafa Bidiyo a shafin sada zumunta watau TikTik domin nuna bajintar da ya yi wajen sauya fasalin Keke mai kafa uku wacce aka fi sani da Keke Napep.
Bidiyon, wanda shafin @nanaadwoakorang ya wallafa ya nuna yadda mutumin ya sauya Keken ta koma kamar Jirgi mai saukar Angulu.
![Keke Napep. Keke Napep.](https://cdn.legit.ng/images/1120/5ecaa9943ff6625b.jpeg?v=1)
Asali: UGC
Sai dai bidiyon wanda ya watsu, bai nuna lokacin da mutumin ya sauya Keken ba, amma ya nuna yadda mutumin ke daukar Fasinjoji yana kasuwancinsa da ita.
![](https://cdn.legit.ng/images/360x203/6364a6c9fc280621.jpeg?v=1)
Kara karanta wannan
An Samu Babbar Matsala: Wasu Jiragen Sama Sun Yi Karo a Sararin Samaniya, Rayuka Sun Salwanta
Bidiyon Keke Napep din da aka sauya ta koma kamar Jirgi
A bidiyon mai tsawon dakika 18, mutumin ya fito cikin jama'a da Keke Napep din kuma mutane sun yi mamakin yadda ta koma.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Har Fasinjojin da ya rika dauka sun gaza boye farin cikinsu bayan samun damar hawa Jirgin Keke.
Mutane da yawa a Soshiyal Midiya sun yaba wa basirarsa ta kirkira, wanda har ya iya tunanin fasaha haka ya sauya Keken ta kayatar.
Bidiyon da aka wallafa a ranar 2 ga watan Janairu, 2023 ya karade Shafukan sada zumunta kuma akalla mutane 908 ne suka duba a TikTok kadai.
Kalli bidiyon a nan
Martanin mutane a Soshiyal midiya
@realbrightobour ya ce:
"Kai jama'a abun mamaki ba zai taba karewa ba, hahahha gunin kyau da kayatarwa."
@emmanueladugyamfi61 ya bayyana ra'ayinsa da cewa:
"Ya Kayatar sosai."
@Wonder boy king Charles ya ce:
"Aiki mai kyau na tafe."
@joy boy tambaya ya yi da cewa:
"Shin wannan mota ce ko jirgin sama."
A wani labarin kuma Wata budurwa ta gina wa iyayen katafaren gina na buga wa a jarida, Hotuna sun ja hankalin mutane
Budurwar ta cika mafarkin da take a rayuwa na ganin mahaifanta suna rayuwa a cikin gidan keta tsara, tace ta dade da burin haka.
A cewarta, sun yi mata komai a rayuwa sannan sun yi aiki tukuru tare da sadaukar mata da abubuwa a rayuwa don haka ta gwangwaje su da wannan alkhairin.
Asali: Legit.ng