PTDF ta fara tantance dalibai 6,000 da za ta tsallakar dasu kasashen waje don karo karatu

PTDF ta fara tantance dalibai 6,000 da za ta tsallakar dasu kasashen waje don karo karatu

Hukumar kula da asususn cigaban kimiyya ta Najeriya, PTDF, ta fara tantance kimanin dalibai 6,000 da suke neman guraben samun tallafin karatu daga gwamnatin tarayya a jami’o’in kasashen waje na shekarar 2020/2021.

A cewar hukumar, fiye da mutane 25,000 ne suka nemi guraben samun tallafin a matakin digiri na biyu Msc da kuma PhD, daga cikinsu ne hukumar ta ware mutane 6,000 wadanda za ta yi ma tamyoyin gaba da gaba da kuma tantancewa.

KU KARANTA: Annobar Lassa ta halaka mutane 8, babban Likita da wani hakimi a jahar Bauchi

Shugaban sashin tallafin karatu na kasashen waje, Bello Mustapha ya bayyana cewa za su dauki tsawon makonni biyu suna gudanar da aikin tantancewar a dukkanin shiyyoyin Najeriya guda shida.

“Muna amfani da kashi 90 na tsofaffin daliban da muka dauki nauyinsu a matakin PhD, kuma suka samu kyawawan sakamako a matsayin wadanda za su yi ma masu neman guraben tambayoyi, ire iren mutanen sun kai 91 da muka dauka don yin wannan aiki.” Inji shi.

Daga cikin kasashen da gwamnatin Najeriya ta kulla alakar fitar da dalibanta zuwa jami’o’insu akwai Farasa, Jamus, China, Birtaniya da kuma kasar Malaysia.

A wani labarin kuma, gwamnatin Najeriya a karkashin jagorancin shugaban kasa Muhammadu Buhari ta dakatar da yunkurin da take yi na ciyo bashin dala biliyan 22.7, kimanin naira tiriliyan 8.3 domin gudanar da wasu manyan ayyuka.

Ministar kudi, Zainab Shamsuna Ahmad ce ta bayyana haka a yayin wani taro da hukumar kula da hannun jari ta Najeriya ta shirya inda tace gwamnatinta fasa karbar bashin ne saboda halin da tattalin arzikin duniya ta shiga a yanzu.

A cewar Shamsuna, koda majalisun dokokin Najeriya sun amince ma gwamnati ta ciyo bashin, a gaskiya ba zasu cigaba da kokarin ciyo kudaden ba, saboda Alkalumman kasuwanci a yanzu sun nuna rashin amfanin ciyo bashin a yanzu.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Online view pixel