Karya Ta Kare, Masu Bincike Sun Gano Abin da Ya Yi Sanadin Mutuwar Matasa 37 a Ofishin NSCDC
- Kwamitin bincike mai mutum 10 ya gano cewa abin da ya yi sanadin mutuwar mutasa 37 da ake zargin masu haƙar ma’adinai ba bisa ƙa’ida ba ne
- Gwamnatin tarayya ta kafa kwamitin ne bayan Shugaba Bola Tinubu ya bayar da umarnin gudanar da cikakken bincike kan lamarin
- Kwamitin ya gano wasu kura-kurai a tsarin hukumomi da kuma wuce gona da iri daga wasu jami’ai
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja, Nigeria - kwamitin bincike mai zaman kansa da gwamnatin tarayya ta kafa domin binciken mutuwar matasa 37 a ofishin hukumar NSCDC na jihar Neja, ya mika rahoto.
A rahoton bincike, kwamitin ya gano musabbabin mutuwar matasan, wadanda jami'an NSCDC suka kama suka tsare a ofishinsu kan zargin hakar ma'adanai ba bisa ka'ida ba.

Source: Twitter
Abin da ya yi sanadin mutuwar matasa
The Cable ta rahoto cewa kwamitin ya gano cewa mutanen sun mutu ne sakamakon shakewa saboda rashin iskar numfashi saboda cunkoso da zafi, lamarin da kan sa mutum ya fita hayyacinsa, ya samu illa a jikinsa ko kuma ya mutu.
Shugaban kwamitin, Jonathan Kure, ne ya bayyana hakan a ranar Talata, yayin da yake miƙa rahoton binciken ga Ministan Harkokin Cikin Gida, Olubunmi Tunji-Ojo, a Abuja.
Gwamnatin tarayya ta kafa kwamitin a ranar 19 ga Satumba, bayan Shugaba Bola Tinubu ya bayar da umarnin gudanar da bincike “cikakke kuma a bayyane” kan mutuwar matasan.
Matakan da gwamnati ta dauka
Tunji-Ojo ya sanar da matakin a cikin wata sanarwa, inda ya kuma bayyana sunayen jami’ai 21 da aka dakatar da su daga aiki dangane da lamarin.
Kwana biyu kafin kafa kwamitin, NSCDC ta ce an kama waɗanda ake zargin ne a yayin wasu samame da aka gudanar a ranakun 15 da 16 ga Satumba a kusa da unguwar Mohammed Inuwa Wushishi Estate da ke Minna, babban birnin jihar Neja.
A cikin wata sanarwa, Kwamandan NSCDC na jihar Neja, Suberu Aniviye, ya ce an samu “mutane da dama daga cikin waɗanda ake tsare da su sun mutu da sanyin sakamakon zargin ɓarkewar wata cuta”.
Bayan faruwar lamarin, gwamnatin tarayya ta dakatar da kwamandan NSCDC na jihar Neja, tare da bayar da umarnin gudanar da cikakken bincike kan yanayin da ya kai ga mutuwar mutanen.
Yadda aka gudanar da binciken
Da yake magana a wani taron manema labarai a Abuja, Kure ya ce kwamitin ya je Minna, ya duba wurin da ake tsare da mutanen, ya gudanar da binciken gawarwaki, tare da tattara bayanai daga jami’an NSCDC, waɗanda suka tsira, iyalan mamatan da sauran shaidu.
Ya ƙara da cewa kwamitin ya kuma tattara takardu da wasu hujjojin binciken kimiyya domin taimaka masa wajen gano gaskiyar abin da ya faru.

Source: Twitter
Kure ya bayyana cewa sakamakon binciken farko ya nuna akwai giɓi a tsarin hukumomi, tare da wuce gona da iri daga wasu jami’ai, kamar yadda Daily Trust ta rahoto.
Ya ce lamarin ya nuna buƙatar jami’ai su ƙara ƙwarewa da bin ƙa’idojin aiki, musamman wajen gudanar da al’amura masu matuƙar muhimmanci irin wannan.
Kwamandan NSCDC ya nemi afuwa
Kun ji cewa Suberu Aniviye, kwamandan rundunar Hukumar Tsaron Fararen Hula ta Najeriya (NSCDC) a Jihar Neja da aka dakatar, ya fito ya nemi afuwa.
Kwamandan na NSCDC ya nemi afuwar iyalan mutum 37 da ake zargin masu haƙar ma’adanai ba bisa ƙa’ida ba ne, waɗanda suka mutu a hannun hukumar.
Asali: Legit.ng

