Uba da ’Da Sun Shiga Magana, an Kama Yaro na Zana wa Babansa Jarabawar Karin Girma

Uba da ’Da Sun Shiga Magana, an Kama Yaro na Zana wa Babansa Jarabawar Karin Girma

  • An kama wani matashi mai shekaru 33 a Abuja bisa zargin rubuta jarabawar ƙarin matsayi ta ma’aikatar Abuja a madadin mahaifinsa
  • Jami’an tsaro sun cafke Mansur Musa yayin da yake rubuta jarabawar mahaifinsa, Musa Mohammed, ma’aikacin hukumar kashe gobara
  • Mahaifin ya amsa cewa shi ne ya tura ɗansa rubuta jarabawar, inda aka miƙa su ga ’yan sanda bayan DSS ta yi musu tambayoyi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abuja - An kama wani matashi mai shekaru 33, Mansur Musa, bisa zargin rubuta jarabawar ƙarin matsayi ta ma'aikatar Abuja a madadin mahaifinsa

Mahaifinsa, Musa Mohammed, ma’aikacin hukumar kashe gobara ta Abuja ne, kuma lamarin ya faru yayin jarabawar ƙarin matsayi da hukumar ke gudanarwa.

Kara karanta wannan

Yadda matashi ya rasa ransa bayan caka masa wuka a Jigawa kan N500 kacal

Yaro ya shiga hannu kan zana wa babansa jarabawar karin girma a Abuja
Mahaifi da dansa da ake zargin sun hada baki domin rubuta wa baban jarabawar karin girma. Hoto: Lere Olayinka.
Source: Facebook

Lere Olayinka, mai taimaka wa ministan Abuja, Nyesom Wike, kan harkokin yaɗa labarai, ne ya bayyana a wani bidiyo da ya wallafa a Facebook.

Yadda aka kama yaro da mahaifinsa

Ya ce jami’an tsaro da aka tura wurin jarabawar da ke harabar Jami’ar Najeriya, NOUN, da ke Abuja, sun kama matashin.

Olayinka ya ce lamarin ya faru ne a rana ta uku na jarabawar ƙarin matsayi da Hukumar Kula da Ma’aikatan Abuja ke gudanarwa.

Ya bayyana cewa Mansur Musa mai shekaru 33 an kama shi ne yana rubuta jarabawar a madadin mahaifinsa, Musa Mohammed.

A cewar Olayinka, da farko matashin ya shaida wa jami’an tsaro cewa mahaifinsa ba shi da lafiya lokacin da suka tambaye shi dalilin halartarsa.

Sai dai ƙarin bincike ya nuna cewa mahaifin nasa ma yana harabar wurin da ake gudanar da jarabawar a lokacin da lamarin ya faru.

Kara karanta wannan

Ministan Tinubu bai ji daɗin abin da ya faru da mutane 32 a jirgin saman sojojin Najeriya ba

Yaro da mahaifinsa sun shiga matsala a Abuja
Taswirar birnin tarayyar Najeriya, Abuja. Hoto: Legit.
Source: Original

Abin da yaron da aka kama ya ce

A cikin wani bidiyo, Mansur ya amsa cewa mahaifinsa ne ya umarce shi da ya zauna ya rubuta jarabawar ƙarin matsayi a madadinsa.

Lokacin da aka tambaye shi shekarun mahaifinsa, Mansur ya ce yana tsakanin shekaru 67 zuwa 68, amma mahaifin ya bayar da wani bayani daban.

Mahaifin ya ce zai cika shekaru 60 a watan Fabrairu na 2027, lamarin da ya bambanta da bayanin da ɗansa ya bayar.

Ya kuma shaida wa jami’an tsaro cewa ya kammala makarantar firamare a shekarar 1977, sannan ya kammala sakandare a shekarar 1982.

Kara karanta wannan

Yadda Tinubu da abokinsa suka kusa fada wa gadar Legas a hadarin mota

Olayinka ya ce mahaifin ya amsa cewa shi ne ya tura ɗansa domin ya rubuta jarabawar a madadinsa, sannan ya nemi afuwa.

Ya ce daga bisani jami’an Hukumar DSS, sun karɓi bayanan mutanen biyu kafin a miƙa su ga ’yan sanda.

An kama mutanen ne yayin da ake ci gaba da gudanar da jarabawar ƙarin matsayi da Hukumar Kula da Ma’aikatan Abuja ta shirya.

Jarabawar na daga cikin shirin ƙarin matsayi da hukumar ke gudanarwa domin ma’aikatan gwamnati da suka cancanta su samu damar ɗaukaka matsayinsu.

An kama mai cin mutuncin malaman Musulunci

A wani labarin, an ji cewa ‘yan sanda sun kama wani mutum da aka ayyana a matsayin wanda ake nema, bisa zargin cin zarafin malaman addini ta kafafen sada zumunta.

An kama mutumin ne bayan wasu limaman addini sun shigar da korafi, inda suka zarge shi da yin kalaman batanci kan su da akidunsu.

‘Yan sanda sun ce za a gurfanar da wanda ake zargin bayan kammala bincike, yayin da ake jiran wasu korafe-korafe domin gano cikakken lamarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jarida ne da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.