An Zo wajen: Gwamnatin Tinubu Ta Amince Cewa Ta Jefa 'Yan Najeriya cikin Talauci
- Daniel Bwala ya amince cewa sauye-sauyen tattalin arzikin gwamnatin Tinubu sun jefa wasu ƙarin ’yan Najeriya cikin talauci
- Ya ce cire tallafin fetur da sauyi a kasuwar canjin kuɗaɗen waje sun haifar da tsadar rayuwa, sufuri da harkokin kasuwanci
- Bwala ya dage cewa duk da wahalhalun farko, gwamnatin Tinubu ta samu gagarumin ci gaba tun bayan fara sauye-sauyen tattalin arzikin
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
FCT, Abuja - Mai ba Shugaban Ƙasa Bola Tinubu shawara na musamman kan sadarwa da manufofi, Daniel Bwala, ya amince cewa sauye-sauyen tattalin arzikin gwamnatin sun ƙara yawan mutanen da ke fama da talauci.
Sai dai Bwala ya dage cewa gwamnatin ta samu gagarumin ci gaba tun bayan fara aiwatar da sauye-sauyen.

Source: Twitter
Cire tallafin fetur ya ƙara tsadar rayuwa
Bwala ya bayyana hakan ne yayin da yake magana a shirin Politics Today na Channels Television ranar Laraba, 7 ga watan Oktoban 2026, inda yake kare sauye-sauyen da gwamnatin Tinubu ta fara aiwatarwa tun bayan hawanta mulki a 2023.

Kara karanta wannan
Dan takarar gwamna ya sadaukar da albashinsa ga matan mazajensu suka mutu idan ya ci zabe
Sauye-sauyen sun haɗa da cire tallafin fetur da kuma haɗa kasuwar canjin kuɗaɗen waje, matakan da suka haifar da ƙarin tsadar rayuwa ga ’yan Najeriya.
Bayan aiwatar da matakan, gidaje da ’yan kasuwa sun fuskanci ƙarin kuɗaɗen sufuri, jigilar kayayyaki da kuma samar da hajojin kasuwanci.
Gwamnati ta ce sauye-sauyen sun zama dole
Gwamnatin Tarayya ta sha kare matakan, tana mai cewa sun zama dole domin gyara matsalolin tattalin arzikin da suka daɗe suna addabar ƙasar.
Ta kuma ce sauye-sauyen na da nufin rage matsin lamba kan kuɗaɗen gwamnati da kuma samar da ingantaccen tsarin tattalin arziki.
A jawabinsa na ranar 1 ga Oktoba, Shugaba Tinubu ya ce hauhawar farashin kayayyaki ya ragu daga matakin da ta kai a baya, yayin da ajiyar kuɗaɗen waje ta ƙaru, kuma kasuwar canjin kuɗaɗen waje ta samu daidaito.
Tinubu ya bayyana Najeriya a matsayin ƙasar da ta kai wani muhimmin mataki na sauya tattalin arziki daga lokacin gyare-gyare zuwa wadata.

Kara karanta wannan
Gwamnatin Tinubu ta fara bayani kan kudin cire tallafin fetur, ta fadi yadda ta kashe $500m
Bwala ya amince da wahalhalun da aka sha
Sai dai Bwala ya amince cewa sauye-sauyen sun jefa mutane da dama cikin matsin rayuwa a farkon aiwatar da su.
“Don Allah bari na bayyana, har ga ’yan adawa, cewa dalilin da ya sa kuke ganin wannan adadi na talakawa da wasu daga cikin hasashe mara kan gado da mutane ke yi shi ne saboda mun aiwatar da sauye-sauye,” in ji shi.
Ya ce babu wata ƙasa da za ta fara aiwatar da irin waɗannan sauye-sauye ba tare da jama’a sun fuskanci wasu matsaloli ba.
“Babu wani wuri a duniya da za ka fara irin wannan sauyi ba tare da samun rashin jin daɗi ba. Mutane da yawa sun ƙara fadawa cikin talauci, mun amince da hakan,” in ji Bwala.
Ya ce an samu ci gaba tun bayan fara sauye-sauyen
Bwala ya ce duk da cewa har yanzu akwai ɗimbin ’yan Najeriya da ke fama da talauci, ya kamata a duba ci gaban da ya ce ƙasar ta samu tun bayan fara sauye-sauyen.
“Amma tun lokacin da aka fara sauye-sauyen zuwa yau, mun samu gagarumin ci gaba, wanda shi ne abin da muka shafe shekaru uku muna gaya wa ’yan Najeriya,” in ji shi.
Ya ƙara da cewa ba za a iya musanta cewa akwai mutane da dama da ke fama da talauci ba, amma a cewarsa, gwamnatin ta samu ci gaba a fannonin tattalin arziki tun bayan fara aiwatar da sauye-sauyen.

Source: Twitter
Dan Arewa ya koma bayan Tinubu
A wani labarin kuma, kun ji cewa fiitaccen mai amfani da kafafen sada zumunta, Al’ameen Yabo, ya sauya ra’ayinsa kan zaɓen shekarar 2027.
Matashin wanda a baya yake tafiyar Atiku Abubakar ya bayyana goyon bayansa ga Shugaba Bola Ahmed Tinubu.
Asali: Legit.ng
