BVN: Sababbin Dokoki 5 da CBN Ya Kawo da Za Su Shafi Asusun Bankin Ku daga Maris

BVN: Sababbin Dokoki 5 da CBN Ya Kawo da Za Su Shafi Asusun Bankin Ku daga Maris

Abuja - Babban Bankin Najeriya (CBN) ya sanar da garambawul ga tsarin lambar tantancewa ta banki (BVN) wanda zai fara aiki daga ranar 1 ga Mayu, 2026.

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Wannan mataki na nufin ƙarfafa tsaron asusun ƴan Najeriya da kuma dakile dabarun da masu damfara ke amfani da su wajen sace kuɗaɗen mutane.

Babban bankin Najeriya, CBN, ya kawo sababbin dokoki ga tsarin BVN
Olayemi Cardoso, shugaban babban bankin Najeriya, CBN. Hoto: Bloomberg/Contributor
Source: Getty Images

BVN: Sababbin dokoki 5 da ya kamata ku sani

Channels TV ta tattaro wasu muhimman dokoki guda biyar da kowane mai asusun banki ya kamata ya sani kafin cikar wannan lokaci yau:

1. Sauya lambar waya sau 1 kacal

A ƙarƙashin sabuwar dokar, mutum yana da damar sauya lambar wayar da ke maƙale da BVN ɗinsa sau ɗaya kacal a tsawon rayuwarsa.

Wannan mataki na nufin magance matsalar "damfara ta sauya lambar waya," inda ɓarayi ke karɓe lambar wayar mutum domin shiga asusunsa na banki. Ana shawartar mutane su tabbatar lambar da suka yi amfani da ita tana da rajista da kuma lamba ta NIN.

Kara karanta wannan

Sunayen manyan jami'an sojin Najeriya da suka mutu a bakin aiki daga 2016 zuwa 2026

2. BVN na masu shekaru 18 ne zuwa sama

Daga ranar 1 ga Mayu, ba za a sake barin yara ƙanana su yi rajistar BVN na kansu ba. CBN ya saita shekaru 18 a matsayin mafi ƙarancin shekarun mallakar BVN.

Iyaye da masu kula da yara za su ci gaba da amfani da asusun ajiya na musamman da aka tsara don yara wajen adana musu kuɗaɗe.

3. Sanya ido kan asusun da ake zargi

Bankuna za su fara sanya kowane asusun da ake zargi da harkallar damfara a wani rumbun bibiya na musamman na tsawon sa'o'i 24.

A cikin wannan lokacin, za a iya takaita hada-hadar kuɗi a asusun yayin da banki ke tuntuɓar mai shi don tabbatar da gaskiyar zargin da ake yu, kamar yadda rahoton Vanguard ya nuna.

4. Wayar salula 1 ga manhajar banki

Daga watan Mayu, ba za a sake barin mutum ya buɗe manhajar bankinsa a wayoyi daban-daban a lokaci guda ba.

Kara karanta wannan

APC ta gamu da koma baya, tsohon shugabanta ya fice daga jam'iyyar

Idan ka buɗe asusunka a sabuwar waya, zai rufe kansa a tsohuwar wayar, sannan za a buƙaci ƙarin tantancewa. Wannan zai hana ɓarayi amfani da bayanan mutum a wasu wayoyin na daban.

5. Hada-hadar ₦20,000 kacal idan aka sauya waya

Duk wanda ya buɗe manhajar bankinsa a sabuwar waya, ba zai iya tura sama da ₦20,000 ba a cikin sa'o'i 24 na farko, a cewar rahoton Arise News.

Wannan dokar za ta kasance kariya ga abokin hulda ko da an sace masa bayanan sirri, domin ba za a iya kwashe masa dukkan kuɗi lokaci ɗaya ba.

Idan abokan hulda da bankuna ba su kiyaye dokokin CBN na BVN ba, za su iya rasa kudadensu.
Olayemi Cardoso, shugaban babban bankin Najeriya, CBN. Hoto: @cenbank
Source: Twitter

Shawara ga masu asusun banki

Kafin ranar 1 ga watan Mayu, yana da kyau mutane su tabbatar lambar da ke jikin BVN ɗinsu ita ce lambar da suke amfani da ita na dindindin.

Haka kuma, duk wanda yake son gyara bayanai, zai fi kyau ya yi hakan yanzu kafin dokar ta fara aiki domin guje wa fuskantar matsaloli a nan gaba.

Hada BVN, NIN da asusun banki

Tun da fari, mun ruwaito cewa, bankin CBN ya umurci duk abokan huldar bankuna da su hada lambar su ta kasa (NIN) da kuma lambar tantance bankin (BVN) da asusun bankinsu.

Kara karanta wannan

DSS ta gano tsohon 'dan majalisa da ya kada hantar Amurka da rashin tsaro a Najeriya

Babban bankin Najeriya ya umurci duk abokan huldar bankuna da su hada lambar su ta kasa (NIN) da kuma lambar tantance bankin (BVN) zuwa asusun bankinsu.

Lambar BVN wata fasaha ce da ke aka samar da ita domin tantancewa tare da adana bayanan mutum da nufin samar da tsaro gare shi a hada-hadar kudi ta bankuna.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com