Kwamacala: An Fasa Auren Saurayi da Budurwa a Jigawa saboda Shugaba Tinubu

Kwamacala: An Fasa Auren Saurayi da Budurwa a Jigawa saboda Shugaba Tinubu

  • Wani abin al'ajabi ya faru a Dutse da ke jihar Jigawa bayan mahafin wata yarinya ya fasa aurar da ‘yarsa ana daf da bikin aure
  • Mutumin ya bayyana cewa shi fa babu abin da saurayin 'yarsa ya yi masa kawai wasu dalilai ne suka sanya shi daukar matakin
  • Matakin ya janyo ce-ce-ku-ce a al’umma, inda wasu ke ganin siyasa na shafar rayuwar yau da kullum na mutane

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Dutse, Jigawa - Rahotanni daga jihar Jigawa sun nuna cewa wani mutum mai suna Sani ya sanar da fasa auren 'yarsa ana daf da biki.

Mutumin daga unguwar Yalwawa a Dutse ya dakatar da shirin aurar da ‘yarsa a saura kwana daya a daura auren saboda Bola Tinubu.

An fasa aure a Jigawa saboda son Tinubu
Shugaba Bola Tinubu, mata da miji a sallar idi a Ikeja da ke Lagos. Hoto: Adekunle Ajayi (An yi amfani da hoton ne domin misali, bai da alaka da labarin).
Source: Getty Images

Jigawa: An fasa aure saboda kaunar Tinubu

Kara karanta wannan

Iran ta harbo jirgin yaƙin Amurka, an sanya ladar kudi ga wanda ya kamo matuƙan

An ce an shirya gudanar da auren a ranar da aka tsara, amma a daren da ya gabata ne mahaifin yarinyar ya sanar da bangaren saurayin cewa ya janye daga yarjejeniyar, cewar Sawaba FM Hadejia.

Majiyoyi sun bayyana cewa wannan mataki ya jefa bangarorin biyu cikin mamaki, musamman ganin cewa an kammala kusan dukkan shirye-shiryen bikin auren.

Bayan shigar dattawa da masu ruwa da tsaki domin sulhu, Malam Sani ya bayyana cewa saurayin bai taba aikata wani laifi kai tsaye a gare shi ba da za a fasa auren.

Sai dai ya nuna damuwarsa ne kan yadda saurayin ke bayyana goyon baya ga manufofin Bola Ahmed Tinubu a shafukan sada zumunta.

Mahaifin amarya ya fasa auren yarsa ga saurayi da ke goyon bayan Tinubu
Taswirar jihar Jigawa da goyon bayan Tinubu ya hana auren masoya. Hoto: Legit.
Source: Original

Abin da dattijon ke zargin saurayin da aikatawa

A cewarsa, irin wannan matsayi na siyasa yana nuna masa wasu halaye da bai gamsu da su ba, ciki har da abin da ya kira rashin tausayi da kuma raunin imani.

Saboda haka, ya ce bai ga dacewar ci gaba da aurar da ‘yarsa ga saurayin ba, duk da kokarin da aka yi na sasanta lamarin.

Lamarin ya haifar da muhawara a tsakanin jama’a, inda wasu ke ganin shawarar ta fi alaka da ra’ayin siyasa fiye da cancantar saurayin.

Kara karanta wannan

An rasa babban Sarki: Ƴan bindiga sun bindige basarake yayin hutawa da matarsa

Wasu kuma sun goyi bayan matakin mahaifin, suna masu cewa yana da ‘yancin yanke hukunci bisa dalilan da ya ga sun dace.

Har yanzu babu wani martani daga bangaren saurayin ko iyalansa, amma masu sharhi na ganin irin wannan lamari na nuna yadda siyasa ke kara shiga cikin harkokin zamantakewa a Najeriya.

Cikon mazaunai ya jawo ango ya fasa aure

A baya, mun ba ku labarin cewa wani ango ya kekashe kasa ya ce ya fasa auren masoyiyar da ya so yin rayuwa da ita saboda ya gano tana amfani da ciko a mazaunanta.

Tsawon lokacin da masoyan suka shafe, angon bai taba ankara da cewar masoyiyar ta sa na yin ciko ba sai da aka zo yin hotunan kafin aure.

Fitacciyar mai ayyukan jin kai, Fauziyya D. Sulaiman ta yi kira ga 'yan mata da su gyara halayensu musamman a kan yin ciko domin hakan ba daidai ba ne.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.